Connect with us

LABARAI

Rashin Muhimmanta Karatun Littafai A Nijeriya Abin Kunya Ne – Nda-Isaiah

Published

on

Batun rashin kwazon ’Yan Nijeriya a bangaren nazarin littafai na cigaba da ci wa masana tuwo a kwarya sakamakon illar da abin ke yi wa cigaban kasar.

Daya daga cikin fitattun marubuta a kasar nan, wanda har ila yau shi ne shugaban Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP da ke wallafa Jaridun LEADERSHIP, Mista Sam Nada-Isiah ya nuna damuwa kan shakulatin-bangaro da ake nuna wa karatun littfai a Nijeriya tare da bayyana lamarin a matsayin abin kunya.

Shahararren marubucin ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da Littafin da Hajiya Amina Abdulmalik Giwa ta rubuta a kan yadda yaran da ke tasowa za su gyara matsalolin da ake cin karo da su na zamani wanda ta sa wa suna “The Wasted Generation”, (Lalacewar Zamani)

Wanda ya shugabanci taron kaddamarwar, Mista Sam Nda-Isiah ya ce ga dukkan alamu Nijeriya ce bababr kasar da ba a damu da kafa katafaran shagunan sayar da littafai ba.

 

“Akwai raggwanci sosai wurin karanta littafai a nan. Watakila Nijeriya ce babbar kasar da a duniya idan ka kewaya ba za ka ga manyan shagunan littafai ba. Idan ka yi tafiya ka zagaya kananan kasashe irin su Singafo, Afirka ta Kudu har da Dubai ma; za ka ga katafaran shagunan littafai a manyan gine-ginensu. Mu ba mu da wannan a nan.

“Ina taya marubuciyar wannan littafi, Hajiya Amina murna kan namijin kokarinta. Matukar kai marubuci ne, za ka yaba da abin da ta yi. Littafin ya rubutu. An yi amfani da kaifin basira. Rubuta kirkirarren labari ya fi caja kwakwalwa a kan duk wani rubutu. Na shawarce ta ta yi wa littafin rajista da Hukumar Kula da Bunkasa Binciken Ilimi ta Kasa (NERDC) domin matasan da ke makarantunmu na sakandare su samu damar karantawa. Littafin ya tabo batutuwan da ke faruwa a zamanin nan. A cikin littafin, matasa za su iya daukar darasin cewa ba sai an bi ta barauniyar hanya ba za a iya samun mafita kan abin da ya addabe su, akwai hanyoyi na daban da za a iya bi. Littafin yana da muhimmanci kwarai da gaske wajen ba da gudunmawa ga matsalar rashin cigaban al’ummarmu.” In ji Mista Nda-Isiah.

Littafin mai shafuka 154, an kaddamar da shi ne a Otel din Chelsea da ke tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Alhamis din nan.

Littafin ya fi mayar da hankali ne wajen bayyana matsalar rashin da’a da yadda abin ka iya haifar da cin hanci da rashawa a wurin matashin Dan Nijeriya.

Da take tsokaci a kan littafin, marubuciyar, Hajiya Amina ta bayyana cewa, “Na kammala rubuta littafin tun a shekarar 1996 amma sai na yi biris da shi. Hankalina ya dawo kan littafin ne bayan mun hadu da Dillibe Onyeama a wurin taron tunawa da Alhaji Abubakar Gimba, inda ya karfafa min gwiwar cewa kar in bari hazakar da nake da ita kan rubutu ta sallace.

“Kuma ikon Allah, wanda muka taru don tunawa da shi din, Alhaji Abubakar Gimba, shi ne ya hada ni da wanda ya dauki nauyin wallafa littafina na farko mai suna “Painful Surrender” (Mika Wuya Mai Daci).

“Littafin ya yi waiwaye ne a kan tsarin da Gwamnatin Buhari da Idiagbon suka aiwatar a yaki da rashin tarbiyya da cin hanci da rashawa daga 1984 zuwa 1985. Idan mutum ya duba littafin, zai fahimci kamarin da rashin da’a ya yi a cikin al’ummarmu. Sai dai kash! Har yanzu ana fama da wannan matsalar ta rashin da’a a tsakanin jama’armu. Takamaime, labarin yana magana ne a kan cin hanci da rashawa da kuma yadda ya kamata al’umma ta gyara domin mu samu cigaba.

“Babban jarumi a littafin, Hannafi ya fito ne daga gidan hamshakai. Babanshi mai kudi ne kuma dan siyasa. Amma sai ya zabi ya zama daban a cikin jama’ar da Allah ya albarkace su da abubuwa masu yawa amma kuma komai nasu a lalace yake. A kokarinsa na lalubo bakin zaren gyara matsalar, sai Hannafi ya yanke shawarar kafa makaranta inda zai rika tarbiyyantar da yara masu tasowa tunda manyan da ake da su sun riga sun lalace”, kamar yadda ta bayyana.

Hajiya Amina ta bukaci kowane mai iyali ya yi kokarin sauke nauyin da ke kansa na tarbiyyantar da ‘ya’yansa ta hanyar cusa musu kyawawan halaye, gaskiya da rikon amana, nuna hazaka da kwazon aiki da sauran su. Ta nunar da cewa wannan ce babbar mafitar dawowa kan tudun-mun-tsira da aka baro a baya da kuma dora manyan gobe a Nijeriya a kan turba tagari.

Wacce ta yi bitar littafin, lara Plugbemi, ta yi bayanin cewa duk da kasancewar an yi rubutun littafin ne tun a shekarar 1996, abin ya fi dacewa da yanayin da ake ciki  a yau fiye da wancan lokacin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: