Connect with us

LABARAI

Rashin Yin Hukunci Mai Tsauri Ya Assasa Karuwar Fyade – Chiza

Published

on

An bayyana cewar, rashin yin hukunci mai tsauri shi ya assasa karuwar laifukan fyade a Nijeriya, domin da hukumomin shari’a sun rike hukunce-hukuncen da a ka tsara tuni wannan bala’in bai yawaita ba.

Shugaban riko na Jam’iyyar PDP a Jihar Neja, Alhaji Garba Umar Chiza, ne ya bayyana hakan kan martanin da ya ke mayarwa ga masu ikirarin kirkiro dokoki dan hukunta masu aikata fyade.
Alhaji Garba Chiza yace Najeriya ce kasar da ko an yi doka bai tasiri musamman ga masu hannu da shuni ko daurin gidi, amma maganar doka ba shi ne muhimmin abu ba, a samar da tsarin shari’a mai inganci da zai iya hukunta duk wanda yai laifi hakan zai taimaka wajen takaitar ayyukan fyade, amma da zaran mutum zai aikata laifi sannan ya samu kariya to yaushe ne gwamnati za ta iya kawo karshen laifuka a kasar nan.
Alhaji Chiza yace yau idan ka dubi kasar Iran, duk wanda aka samu da laifin fyade ko dan waye shi za a sare mashi kai ne, ka dubi kasar Tanzaniya suna da dokoki masu tsari da in ma wani ake samu idan aka yi fyade ko cewa mutum kayi ya aikata zai ji tsoron aikatawa saboda hukuncin da zai fuskanta, dan duk wadannan zantuttukan da ake tada jijiyar wuya akan su in har da gaske ake a karfafa guiwar hukumomin shari’a da dokoki bai daya, dole masu aikata fyade za su ji tsoron aikatawar.
Amma yau saboda lalacewar al’ummar mu har gidan mutum za a kwankwasa a yi wa ‘yarsa fyade da iyalin shi a gaban shi kuma idan an kama masu laifin har wai wasu su zo suna kare su, shi ya Allah ba zai jarabce mu ba.
Ya kamata kowa ya ji tsoron Allah, mu sani muddin ka bata ‘yar wani da karfi, uwa ce kuma matar wani ce Allah ba zai barka ba.
Ina kiran gwamnati da hukumomin shari’a, lokaci yayi da za a samar da dokokin ba sani, ba sabo da ganin an takaita aikata laifuka a kasar nan.
Domin idan gwamnati ko hukumomin shari’a da aka dorawa nauyin za su yi hukuncin da ya dace, dole jama’a su ji tsoron aikata fyade ga kananan yara har da manya, domin ko yanzu muna da wasu tanade-tanade a dokokin kasar aiki da su ba ayi shi yasa ka ke ganin laifukan na kara yawaita a kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: