Tun da aka nada shi a matsayin karamin Ministan Tsaro a 2023, Dakta Bello Matawalle ya sake kawo sabon dabaru ta fannin tsaro, nazari da kuma daukar matakan da suka jibi dasa tubalin ginin sashen tsaro na kasa.
A lokacinsa an samu manyan nasarori a bangaren yaki da ta’addanci, zamanantar da rundunar soja, da kuma tabbatar da zaman lafiyar kasa, wadanda sune suka sa ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan mutunen da suke bayar da muhimmiyar gudummawa wurin yaki da rashin tsaro.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Gwamnati Na Ƙoƙarin Tsoratar Da Ni Don In Shiga APC – Sanata Tambuwal
A lokacin jagorancinsa ne Ma’aikatar Tsaro ta samu manya-manyan nasarori domin kawo zaman lafiya a kasa. Wadannan nasarori su ne:
1. Nasarori a kan ta’addanci da satan mutane
Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye.
2. Kula da walwalar sojoji da karfafa musu gwiwa
Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta hanyoyin walwalar sojojin ta hanyar biyan su kudin alawus a kan lokaci, kyautata matsuguninsu, da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya. Wannan ya kara azama wa sojojin da suke gwabza yaki a fagagen fama.
3. Zamanantar da Dakarun Sojoji
Ganin bukatar gaggawa da ke akwai na zamanantar da sojojin Nigeriya, Matawalle ya samar da waraka ta hanyar samar da sabbin makamai na zamani, da jirage marasa matuki don tattara bayanai da kuma kayan ayyuka da sojoji ke bukata lokacin yaki.
Wadannan kayayyaki sun inganta dabarun da sojoji ke amfani da su ta hanyar raguwar yawan sojojin da ke rasa rayukansu da kuma karuwar nasarori a duk lokacin da aka fita ba-ta-kashi.
4. Raguwar sace-sacen mai da zagon kasa wa tattalin arziki.
Tattalin arzikin Nijeriya ya jima na fama da illar da ake masa sakamakon satan danyen mai a yankin Niger Delta. A karkashin jagorancin Matawalle, an samu karuwar aikace-aikacen da suka hada da hadin gwiwar sojojin ruwa wadanda suka hada da lalata cibiyoyin sace danyen mai wanda hakan ya haifar da aruwar danyen mai da ake fitar da kuma karin kudaden shiga ga kasa.
5. Karfafa mu’amala da hadin gwiwa a yankin Afrika da kasa-da-kasa.
Yawancin matsalolin tsaro ya kan wuce iyakar kasa, saboda haka ne Dakta Matawalle bai yi kasa a gwiwa ba wurin daukar matakan kulla kawance da makwabtan asashe irin su Chadi, da Nijar da Kamaru, da sauran kawayen kasashe irin su Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai wanda ya inganta yanda ake tattara bayanai da kuma musayar bayanan sirri. Hakan ya sa ‘yan ta’adda da masu aikata muggan laifuka ke samun wahalar samun maboya.
6. Karfafa kere-keren kayan yaki a gida
Bisa umurnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na tunanin dogaro da kai a fannin tsaro, Dakta Bello Matawalle ya yi kokarin agaza wa Hukumar Samar da Kayan Yaki ta Nijeriya (DICON) domin kara samar da makaman yaki a gida Nijeriya. Wannan mataki ya rage dogaro da kasashen waje da kuma karfafa tattalin arzikin tsaron Nijeriya.
Baya ga bangaren yaki, Bello Matawalle yana cigaba da jaddada muhimmancin aiki da al’umma domin dawo da tsaro. Wannan kiranye da yake yi wurin neman tattaunawa, da sasanci da kuma ayyukan cigaba a yankunan da ake rikici sun taimaka matuka gaya wajen dinke rashin yarda tsakanin jami’an tsaro da kuma fararen hula, wanda hakan zai haifar da zaman lafiya mai dorewa.
Jagorancin Bello Matawalle ya nuna aiki ba kama kafar yaro, sabbin dabaru, da kuma kishin kasa. Nasarorinsa ya nuna irin fahimtarsa a matsalolin tsaron Nijeriya da kuma irin niyyar da gwamnati ke da shi wurin magance su.
Bashir Aliyu dan jarida ne mai nazarin al’amuran da suka shafi siyasa da tsaro.