….Ci gaba daga makon jiya
A karshen tattaunawa da fitaccen jarumin fina-finan hausa cikin masana’antar Kannywood HARUNA TALLE MAI FATA, za ku ji yadda ya yi kira ga gwamnati game da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, bugu da kari jarumin ya ja hankalin masu yunkurin shiga cikin masana’antar Kannywood, hadi da yin kira ga wadandk ke cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Abokina a masana’antar Kannywood guda daya ne, sunanshi Ali Ibrahim Dawayya.
Da wa ka fi so a hada ka a fim, ko ka fi son yin fim da shi?
Ali Dawayya shi ne dai wanda na fi so a hada ni a fim.
Kun taba yin fim tare?
Eh! Mun taba yin fim da shi, amma fina-finan da muka yi ba wai irin wanda nake so ace mun fito sosai da shi bane, shiyasa yanzu nake sha’awar hakan.
Ko kana da ubangida a cikin masana’antar?
Ni ba ni da wani ubangida a cikin masana’antar Kannywood, saboda idan na ce ina da ubangida kamar na yaudari kaina kenan, ubangida shi ne wanda zai rinka kiran ka yana saka ka a fim, sannan yana dora ka a layi, yi kaza bar kaza, yaya kake ciki?, da sauransu. Gaskiya babu, kuma hakan ba wai girman kai bane cewar ba ni da ubangida, magana ta gaskiya ce, ni ba ni da wani ubangida a masana’antar Kannywood.
Ka fin ka fara fim wanne jarumi ko jaruma ce ta fi burge ka, ko ya fi burge ka, kuma me ya sa?
Hafsat Shehu ita ce ta fi burge ni sosai, saboda idan tana fim maganarta ne kadai take burge ni, kuma nayi burin a lokacin nake masana’antar Kannywood da na ta yin fina-finai da ita. Dan ba zan manta lokaci da ta zo garinmu ba, musamman na tashi na tafi ‘location’ dinsu, kowa na dan tsaitsayawa na je wajen haske da ke da daddare ne, ta zo na ganta na ji dadi muka gaisa da Ahmed S. Nuhu, na juya na tafi abina.
Wadanne Jarumai ka fi so su fito matsayin iyayenka a fim?
A maza gaskiya ina son kowa ya fito a Babana, a mata kuma akwai Zainab Unguwar Rogo har mamana ake ce mata, ina son ta fito a mamana saboda tana ba ni abin da nake so, ita nake son ta fito mahaifiyata a duk fim din da muka fito da ita.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka, wanda ba za ka taba mantawa da shi a rayuwarka ba?
Abin da ba zan manta da shi na farin ciki a rayuwata ba, watarana na dawo daga aiki mun yi tafiya da wannan abokin nawa Ali Dawayya, raina a bace yake a lokacin ba zan iya fadar sunan wanda ya batan rai ba, na shiga masaukinmu na soma bacci, sai na ji kiran wani bawan Allah Sheikh Yahaya ina kiransa da Sheikh, sai ya kira ni ya ce “Ka ci gaba da addu’a an biya maka Makkah za ka tafi”, wallahi daga farin cikin nan kawai sai na ga hawayen farin ciki ya fara zuwar mun duk da bakin cikin da nake ciki, ba zan iya manta wannan abun da Sheikh Imamu Abubakar Bala Gana Daraktan Ilimi na Jibwis Nageriya reshen jihar filato ya biya mun. Bayan ya fadan hakan na tashi nayi Sallah na gode wa Allah, dan na riga na san in har aka ce Sheikh Bala Gana ya yi magana to ta tabbata kawai in har Allah ya yarda. Da safe na tashi ina shauki, an ce a boye nema a bayyana samu, dan haka ban fadawa kowa ba, kawai sai ga kiranshi ya ce mun kana da fasfot? , ka je Bauchi ka ce a yi maka ‘passport’, in ka je kar ka bada ko sisi kawai dai kayi kudin mota ka je, sai na ce ina da fasfot, sai ya ce “To! zan turo Abdullahi ya zo ya karba”, kawai sai ya turo babban dansa bawan Allah Abdullahi ya zo ya karbi ‘passport’ dina, ba zan manta da wannan ba, dan akwai abin da ya taba gifta mun dalilin passport ya sa ban je ba, duk da na biya wa mahaifiyata, ta jajje ma, amma ni ban je ba sai gashi Sheikh Abubakar Ibrahim Bala Gana ya biya mun na je, wannan abun ba zan manta da shi ba, na je Raudar Manzon Allah (s.a.w) sanadiyyarsa na yi wa iyayena addu’a shi ma na yi masa addu’a, na je dakin ka’aba na yi wa iyayena addu’a, na yi masa addu’a.
Wanne abu ne ya fi saurin saka ka farin ciki?
Na ganni ina wajen sana’a ta, ko ina yin aikin da wadanda nake so nayi, ko ana yi ana raha kin san fim ana yi ana raha, hakan yana saka ni nishadi.
Misali a ce ‘yar ka ta girma tana sha’awar shiga harkar fim, shin za ka amince ka barta ta shiga ko kuwa ba kada ra’ayin haka?
Eh! toh idan ita ta zabarwa kanta ba ni da zabi, amma in zabi na ne kawai tayi aure, ko ni duk macen da ki ka gani a fim, duk mace indai a fim ne wallahi sai dai in na ga kina yi na saka ki, ban taba samun mace kawai na zo ko ta zo ta same ni na saka ta ba, dan ko yanzu haka akwai mutane da yawa da za su zo su same ni su ce suna son su yi fim mata da sauransu, ina ce musu gaskiya ni bana dauka, ni a kamfani na bana daukar sabuwar jaruma, ko mazan ma ni ban cika dauka ba, amma in ra’ayina ne daga ta girma tayi aure, amma in ta zabawa kanta ita ga abin dk take so kin ga wannan kuma ba ni da zabi.
Wanne irin abinci da abin sha ka fi so, kuma wanne irin kaya ka fi son sakawa?
Shinkafa da Wake da Mai da Yaji, sai Dan Wake, sai Kunun Gyada, kuma Kunun Gyadar ya zama akwai Gyada da zan zuba a ciki, sai kuma dogayen kaya, irin ‘half’ Jamfa da Hula.
Ya alakarka take da sauran abokan aikinka?
Ina zaman lafiya da kowa ba ni da wani abokin gaba a Kannywood.
Bayan sana’ar fim da ka ke yi a yanzu, shin kana wata sana’ar ne?
Ina sana’ar siyar da fata, ina gwangwan din robobi.
Wacce shawara za ka bawa masu kokarin shiga masana’antar Kannywood, har ma da wadanda suke ciki?
Wanda suke kokarin shiga masana’antar Kannywood abin da zan fada musu shi ne, dole in mutum zai shiga ya tsaya ya bi canel din da ya kamata ya shiga, duba da yanzu makaryata sun yi yawa, wani mutumin ma zai iya zuwa ‘location’ saboda mu ‘yan fim kowa namu ne, ko ya ganka a hanya ku yi hoto, in kun yi hoto daga nan shikkenan sai ya rinka ce musu musamman mata “za mu sa ku a fim”, kuma na yi imani har ga Allah duk wanda ya dauki sana’ar nan sana’a ba zai yi wa mace karya ya ce “ki zo zan sa ki a fim” kuma karya yake yi ba. Na farko a samu a yi karatu saboda in ba karatu babu yadda za a yi a shiga, na biyu; mutum ya tabbatar da ina zai je ya shiga? Sai kuma wadanda suke ciki ya kamata su hada da wata sana’ar, in mutum yana wannan ya hada da wata saboda rike sana’a daya musamman fim gaskiya akwai hadari tunda sana’a ce wadda babu fansho babu giratuti, iya aikin da kayi a lokacin za a biya ka, in an biya ka in ba a sake kiranka ba shikkenan, toh idan ba kada sana’a ka rike iya sana’ar fim lokacin da babu ita ko kuma tsufa ya zo ko ciwo ya zo sai a ga an samu damuwa, amma in an hada wasu sana’o’in sai a ga abun ya zo da sauki, Allah ya sa mu dace.
Ko kana da wani kira da za ka yi ga gwamnati game da harkar fim?
Yana da kyau yadda masu harkar fim suke bawa gwamnati gudunmawa, su ma su rinka bata gudunmawa idan sun ci zabe, duba da yadda tun daga kan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ‘yan fim suka bada gudunmawa me yawan gaske, kuma har gwamnatin ta kare ba ta waiwayi masana’antar da kyau ta tuna mana wani abu da za mu rinka yi ba, tunda yanzu masana’antar fim idan ki ka kula za ki ga tana tangal-tangal, ba mu da wani hanyar da in mun yi fim din kudi ya ke dawowa. Toh! da gwamnati za ta duba lokacin Goodluck aka bawa makwabtanmu giran wa fim, to mu ma a bamu haka, sa’annan a gina mana sinimomi, ina ganin da mun ji dadin hakan, kuma da mun ji karfi wajen kara tallata gwamnati, wannan shi ne shawarata ga gwamnati.
Me za ka ce da masoyanka, masu kallon fina-finanka?
Ina sonsu fiye da yadda suke so na, sabida na riga na sani idan babu su to babu ni, ina sonsu kuma ina so su ci gaba da kallon fina-finai na, kuma duk wanda ya ke son kallon fina-finai na, za su iya ziyartar You tube kan Channel me suna MAI FATA HAUSA TB, anan nake saka sabbin fina-finai na kamfani na.
Me za ka ce ga makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Duk wanda ya karanta hirar nan sai na ce na gode Allah ya saka da alkhairi, inda na yi kuskure ina roko a yafe mun, inda na fada daidai kuma Allah ya sa mu dace.
Me za ka ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP Hausa?
Jaridar Leadership Jarida ce mai kyau mai kuma kokari, saboda ma’aikatan suna kokari sosai, kuma na ji dadin kasancewata a jaridar wanda gashi na yi hira a gidan jaridar yau, na ji dadi sosai, kuma zan iya cewa Allah ya saka musu da alkhairi daga ma’aikatan har masu gidan jaridar.