ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Haaland Ya Zura Kwallaye 100 A Firimiyar Ingila

by Abba Ibrahim Wada
9 months ago
Ƙwallaye

Matashin dan wasa Erling Haaland ya doke tarihin Alan Shearer na zura kwallo 100 a raga a gasar Premier League da mafi karancin wasanni ya kuma yi wanan bajintar a wasan da Manchester City ta doke Fulham a filin wasa na Craben Cottage.

Dan wasan dan kasar Norway, mai shekara 25, yana taka rawar gani a kakar bana ta 2025 zuwa 2026, wanda ya zura kwallo 20 a wasa 19 a dukkan wasanni kawo yanzu.

Yanzu dai dan wasa Haaland ya zura kwallo ta 100 a gasar Premier ranar Talata a Craben Cottage, amma za a ci gaba da lissafin ya zura na 101 da na 102 tun da har yanzu zai ci gaba da yin gasar. Ya kuma buga kwallo ta bugi turke har karo biyu a wasan da Fulham, sannan ya bayar da biyu aka zura a raga.

ADVERTISEMENT
  • Lacazette Ya Koma Lyon Daga Arsenal
  • Da Gaske Arsenal Ta Kawo Karfi?

Haaland ne kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar Premier, inda yake da kwallo 15 a raga a kakar nan, yayin da dan wasan Brentford, Igor Thiago ke biye da shi, mai 11 a raga.

Tun bayan da ya koma Manchester City daga Borussia Dortmund a 2022, ya kafa tarihin bajinta da yawa a Ingila, ciki har da doke kwazon tsohon dan wasa Alan Shearer na cin kwallo 100 a wasanni 111.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Sai da dan wasa Alan Shearer ya buga wasanni 124, sannan ya zura kwallo ta 100 a gasar, sannan tsohon kyaftin din tawagar Ingila ya ci 260 a matakin shi ne kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar ta Ingila, wadda daga shekarar 1992 zuwa 1993 aka sauya mata fasali.

Haaland ya koma Manchester City kan fam miliyan 51 a kakar 2022, bayan kaka biyu da rabi a Borussia Dortmund mai buga Bundesliga, inda ya ci kwallo 62 a wasa 67 a Jamus. Kwazon dan wasan mai shekara 25 tun bayan da ya koma Premier League ya dara duk wani mai buga gurbin cin kwallaye a babbar gasar ta Ingila.

Haka kuma shi da kansa ya tashi tukuru da ya samu damar yin wannan bajintar ta cin kwallo 100 a gasar Premier a kaka uku da yake buga wasannin. Kawo yanzu a kakar wasa ta 2025 zuwa 2026, Haaland ya zura kwallo 15 a raga a wasa 14 a Premier League, kuma 20 jimilla a dukkan fafatawa daga wasanni 19.

Da yake kwantiragin tsohon dan wasan Molda da Salzburd zai kare a Etihad a karshen kakar 2034, watakila ya doke tarihin Alan Shearer a karo na biyu, wanda shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Premier League, inda yake da kwallaye 260 jimilla.

Ƙwallaye
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Kula Da Lafiya A Matakin Farko: Zamfara Ta Yi Fintinƙau

Kula Da Lafiya A Matakin Farko: Zamfara Ta Yi Fintinƙau

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.