Dan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri ba zai buga sauran wasannin kakar wasa ta bana ba sakamakon raunin da ya ji a kafarsa.
Dan wasan mai shekaru 28, ya samu rauni ne a wasan da suka tashi 2 da 2 da Arsenal a ranar Lahadi a gasar Firimiyar Ingila, bayan da sun yi karo da Thomas Partey.
- Mace-mace Sakamakon Ibtila’o’in Da Ke Faruwa A Arewa
- Ya Kamata Gwamnati Ta Kula Da Marayun Da Aka Bari Sanadin Mummunan Hatsarin Motar Lere – Sharif Danlami
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yanzu an yi wa Rodri tiyata a gwiwarsa kuma ba zai buga sauran wasannin wannan kakar ba.
“An yi masa tiyata a safiyar yau saboda haka wannan kakar ta kare a wajensa sai dai zai buga kakar gaba,” in ji Guardiola.
Guardiola ya ce Rodri ya kasance dan wasan da ba za a iya maye gurbinsa ba a lokacin gasar cin kofin bara, inda City ta doke Arsenal kuma ta lashe kofin gasar Firimiya karo na hudu a jere.
A cikin wasanni biyar da Rodri bai samu bugawa a kakar wasannin bara ba City ta sha kashi a hudu daga cikinsu,hakan ya sa ake ganin City za ta sha wahala kafin ta murmure daga raunin da Rodri ya samu.