Ronaldo Zai Ci Gaba Da Zaman Juventus – Nedved

Ronaldo

Daga Abba Ibrahim Wada

Daraktan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Pabel Nedved, ya bayyana cewa har yanzu Cristiano Ronaldo bai bayyana wata alamar cewa zai bar kungiyar kwallon kafa ta Juventus ba, kuma ana sa ran dawowarsa bakin aiki nan gaba a wannan watan,.

Nedved ya bayyana cewa kawo yanzu  Cristiano hutu ya ke, kuma babu wata alamar da dan wasan mai shekaru 36, wanda saura shekara daya kwantiraginsa da kungiyar ya kare ya bayyana musu da ke nuni da cewa zai yi hannun riga da su saboda haka suna fatan zai dawo hutu domin ya ci gaba da buga wasa.

Ana bayyana shakku a game da makomar dan wasan, bayan da suka kammala kakar wasa mai sarkakkiya, inda Juventus ta gaza lashe kofin Serie A bayan shekaru  9, aka kuma yi waje daga gasar zakarun nahiyar Turai a matakin kungiyoyi 16, sannan ta karkare kakar a matsayi na hudu, kuma a rana ta karshe.

Tsohon dan wasan na Czech Republic, Nedved ya ce lallai Juventus ta yi murnar kammalawa a mataki na hudu a karshen kakar wasa fiye da yadda ta yi murnar lashe gasar Serie A tare da Maurizio Sarri a shekarar 2020.

 

Exit mobile version