An sami rudani a yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ki amincewa da shugabancin sabuwar jam’iyyar hadaka ta ADC wacce tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark yake jagoranta.
Rahotoni sun nuna cewa shahararrun ‘yan siyasa ne suka amince da ADC a matsayin jam’iyyar adawa da za ta kalubalantar APC da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Hadakar jam’iyyar ta kuma amince da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark, da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban riko kwarya da sakatareta na kasa.
Wasu daga cikin sanannun mambobin jam’iyyar hadakar a wajen taron da aka yi a Abuja, sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsofaffin gwamnonin jihojin Kaduna da Ribas, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da dai sauransu.
Sai dai kuma INEC ba ta lissafa sunayen sabbin kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar ba, ciki har da Mark da Aregbesola a shafin adireshinta na internet ba, wanda lamarin ke ci gaban da janyo muhawara.
Mambobin kwamitin zartarwar na ADC da suka hada da Bolaji Abdullahi (Sakataren yada labarai na kasa), Babachir Lawal (Mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa maso gabas), Usani Uguru Usani (Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa), Farfesa Oserheimen Osunbor (Babban lauyan jam’iyyar na kasa), Bar Chinedu Idigbo (Sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na kasa), Sen. Musa Elayo (Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasar waje) da Kwamared Nkem Ukandu (Sakataren jin dadi da walwala na jam’iyyar na kasa) da sauransu.
Duk da haka, INEC ba ta ki amincewa da sabbin shugabannin tare da kin saka sunayensu da hotunansu a shafinta na yanar gizo. Wannan lamari na ci gaban da damun mambobin jam’iyyar da magoya baya, yana nuna matsaloli a cikin jam’iyyar kafin 2027.
Sai dai yayin da yake mayar da martani ga wannan lamarin, sakataren yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya shaida cewa INEC na bin ka’idojin aikinta ne, yana mai jaddada cewa za a warware rudanin a wannan makon.
Abdullahi, wanda ya kasance tsohon minista ya ce, “Abin da ke faruwa kawai shi ne bin ka’idoin aiki, hakika babu wani abu a ciki. Muna bukatar mu aika da wasu sa hannun kuma komi zai yi daidai.
“Jinkirin yana da alaka da ka’idojin gudanarwa ne kawai. Babu batun siyasah ko wani abu. Kawai yana da alaka ne da ka’idodin gudanarwa kuma za a shawo kan wannan lamari. Jinkirin yana da alaka da hanyoyin aiki kawai kuma zan iya gaya maka cewa a shawo kan lamarin a cikin wannan makon.”
Tun lokacin da aka kirkiri hadakar, shugabancin jam’iyyar yana ta samun suka tare da fadawa cikin rikice-rikice da ke tasowa a cikin jam’iyyar.
Masana sun cewa da tun lokacin da aka kafa kwamitin zatarwa karkashin jagorancin Mark, tsohon dan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu, ya kalubalanci kwamitin tare da bayyana Dabid Mark a matsayin shugaba na kawo rarrabuwar kai a jam’iyyar.
Yayin da yake tattaunawa da ‘yan jarida, Kachikwu ya zargi cewa an tilasta wa Mark zama shugaban wani bangare na ADC.
Kachikwu ya ce rashin adalci ne ga ‘yan Nijeriya a ce Atiku da Aregbesola da Mark su jagoranci hadakar jam’iyyar.
“Wannan wata barazana ce ga ‘yan Nijeriya da kuma mambobin jam’iyyar su kira Dabid Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC. Ba shi ba ne shugaba. Ba zai iya zama ba. Mutanen da suka shigo jam’iyyar ta barauniyar hanya bai kamata su shugabanci jam’iyyarmu ba. Ba za mu kasa a gwiwa ba, duk da irin yakarmu da ake yi,” in ji shi.
Hazlika, tsohon dan takarar gwamna na ADC a Jihar Gombe, Nafiu Bala, ya bayyana cewa fatawar jam’iyyar a hannun Mark da Aregbesola ya saba wa dimokuradiyya kuma ya yi alkawarin yin gwagwarmaya a kan yakar lamarin.
Ya zargi Nwosu da sauran tsofaffin shugabannin jam’iyyar kan watsi da nauyin da aka dora musu kan tafiyar da harkokin jam’iiyyar kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Haka kuma Bala ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar ADC na wucin gadi tun da Nwosu ya yi murabus.
A yayin da yake mayar da martani ga wannan lamari, Nwosu ya shaida wace cewa rikicin shugabanci a jam’iyyar shiryayyan abu ne, yana zargin cewa akwai wadanda suke yin aiki ga fadar shugaban kasa, wanda yanzu suna cikin tashin hankali game da ADC.
“Zan ba da shawara ga ‘yan siyasa su mai da hankali kan bayar da ribar dimokuradiyya ga mutanensu, sannan su shirya don zabe mai zuwz maimakon lalata tsarin zabe ta haramtacciyar hanya,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp