Connect with us

LABARAI

Sama Da Biliyan Bakwai Hukumar Kwastan Ta Kano Da Jigawa Ta Tara A Rabin Shekara -Abba Yusif

Published

on

A kokarin da hukumar Kwastom Kano da Jigawa keyi na tsaftace iyakokin Kasar nan, Shugaban hukamar Kwastom reshen Kano da Jaigawa Alhaji Yusif Abba Kasim ya bayana nasarorin da suka cimma a cikin watannin shida na farkon shekara ta 2018, Kwanaturolan ya bayana haka ne a lokacin taron manema labarai a helkwatar hukumar  dake Kano kamar yadda aka saba gudanar da irin wannan taruka alokaci irin wannan.

Alhaji Yusif Abba Kasim ya bayana cewa hukumar Kwasstan ta kasa ta ba da umarnin  tara abin da ya kai Naira Biliyon7,389,024,423.42 a cikin watanin shida na farkon wannan shekara, ya ce muna yiwa Alah godiya tare da yabawa jami’anmu bisa jajircewar da suka nuna wanda wannan kokari na jami’an  namu ne ya sa muka  samu nassarar tara abin da ya kai Naira Biliyon 8,070,570,235.37, wanda hakan ke nuna mun tara abin da ya haura wanda Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin tarawa da Naira Miliyon 681,545,811.95, Ya ce  babu shakka wannan ba karamar nassara ba ce da muka samu a wannan shiyya ta Kano da Jigawa.

Hakazalika Abba Yusif ya ci gaba da cewa a kokarin da muke na kara ingantawa tare da tsaftace kan iyakokinmu, mun samu Nasarar gudanar da wasu kame kame na wasu haramtattun kaya da suka kai guda 74, sannan kuma mun  kama kayan da ba’a cika ka’idar biyan kudaden fitonsu ba, wanda kudinsu ya kai Naira Miliyon 266,944,264.00.

Kamar yadda na fada ambatawa tunda farko, cikin abubuwan da muka samu Nasarar damkewa sun hadar da motoci guda 41, shinkafar kasashen waje buhu 8,677, Katan 884 na Taliya, Man girki na kasashen waje Jarka mai daukar da lita 25 wanda yawan sa kai 1,955, Tufafin Gwanjo Dila 29, sai Katan 24 na Sabulu, da buhu 103 na Sukari,  da wasu buhuna da aka taba amfani dasu guda 11 da kuma Takalman Gwanjo guda 788.

Da yake karin haske kan kayan da suke kamawa ya bayyana cewa sun kan bukaci duk wanda ke da wani korafi kan ire iren wadannan kaya da cewar kayansu ne su zo su tabbatar da hakan, hak kuma ya bayyana cewa duk abin da suka kama na gwamnati ne ba namu ba ne. Saboda haka kwanturolan ya jaddada bukatar da ake da ita na jama’a su fahimci cewar jami’an hukumar Kwastan na yin aiki ne domin tabbatar da ci gaban harkokin fito, sannan kuma ya kara jan hankalin ‘yan Kasuwa da kowa ya yi kokari bin doka da oda wanda yin hakan ke karawa wannan kasa idon duniya.

 




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: