Kamfanin Moonshot AI, mai sarrafa fasahar AI a kasar Sin, ya sanar a ranar Litinin da ta gabata cewa, zai kaddamar da amfani da Kimi K3 a tsakanin jama’a, wato wani sabon samfurin kirkirrarriyar basira ta AI da kamfanin ya samar.
Samfurin, mai kididdigar dabarun koyo da fahimtar bayanai triliyan 2.8, ya zama samufurin AI mai budadden tsari mafi girma a duniya.
Yayin da samufuran AI masu budadden tsari da kamfanonin Sin ke kirkira suke kara samun bunkasa, fasahar AI tana fita daga dakin gwaje-gwaje cikin sauri inda take samun karbuwa a cikin bangarorin tattalin arziki na zahiri kamar masana’antu, makamashi, ayyukan ba da hidima, wanda ke zama sabon injin habaka sauye-sauyen masana’antu da rage farashin harkar kasuwanci. (Safiyah Ma)














