ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyun Adawa Sun Samu Rarrabuwar Kai Kan Fitar Da Ɗan Takara Guda Da Zai Ƙalubalanci Tinubu

by Sulaiman
1 month ago
Tinubu

Shirin ƴan adawa na haɗa kai wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda da zai ƙalubalanci Shugaban ƙasa, Bola Tinubu a zaɓen 2027 ya samu rabuwan kai, yayin da manyan jam’iyyun adawa suke ɗauki matsayi daban-daban kan tsarin da aka tsara.

Ko da yake ɓangaren jam’iyyar PDP da Tanimu Turaki ke jagoranta ya nuna yiwuwar buɗe ƙofa kan lamarin, yayin da ɓangaren PDP da Nyesom Wike ke jagoranta ya toshe ƙowar kowace irin haɗin gwiwa.

Haka kuma, ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya tabbatar cewa jam’iyyun adawa sun riga sun fitar da ƴan takararsu amma suna ci gaba da dagewa kan yin aiki tare.

ADVERTISEMENT

Duk da haka, APC ta yi watsi da matakin jam’iyyun adawa na dakatar da ita daga lashe zaɓen 2027.

A ranar 25 ga Afrilu, shugabannin jam’iyyun adawa sun haɗu a wani taro a Ibadan, Jihar Oyo, inda suka yanke shawarar aiki tare a zaɓen 2027 da kuma duba yiwuwar fitar da ɗan takara guda ɗaya na shugaban ƙasa don ƙalubalantar Tinubu.

LABARAI MASU NASABA

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Daga cikin shugabannin jam’iyyun adawa da suka rattaba hannu kan lamarin sun haɗa da tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark na jam’iyyar ADC da Tanimu Turaki (SAN) na PDP da Hakeem Baba-Ahmed na PRP da Ajuji Ahmed na NNPP da Cleopas Moses na NDC da Uche Nnadi na APP da Mgbudem Maɗwell na AP.

Sauran sun haɗa da Yusuf Dantalle na APM da Adekunle Omoaje na AA da Samuel Memeh, Abdulrahman Abubakar na YPP da Yabagi Sani na ADP da kuma Dan Nwanyanwu na ZLP.

Taron ya samu halartar fitattun ƴan adawa, ciki har da Atiku, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, tsohon Gwamnan Jihar Kurus Ribas, Liyel Imoke da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal.Kusan watanni uku bayan taron Ibadan, wasu daga cikin shugabannin da suka halarci taron sun fito a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa ko mataimakan ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa daban-daban.

Atiku da Amaechi sun fito a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa na ADC, yayin da Makinde ya fito a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APM. Haka kuma, Obi da Kwankwaso sun bayyana a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa na NDC, yayin da wasu mahalarta taron suma suka samu tikitin takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyun adawa daban-daban.

Biyo bayan ranar ƙarshe ta 30 ga Mayu da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta saka wa jam’iyyun siyasa domin gudanar da zaɓen fitar da gwani na ƴan takararsu, jam’iyyun sun kammala aikin tun daga wannan lokaci kuma suka saka sunayen ƴan takararsu a shafin INEC.

A yayin da yake magana kan lamarin, sakataren yaɗa labarai na kwamitin gudanarwa na PDP da Turaki ke jagoranta, Ini Ememobong, ya bayyana cewa shirin jam’iyyar adawa na gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya don ƙalubalantar Tinubu har yanzu yana nan kuma lamari ne da za a iya cimmawa.

Sai dai ɓangaren PDP na Wike ya ƙaryata rahotannin haɗin gwiwa da kowace jam’iyya ta siyasa kafin babban zaɓe, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na shirin yin takara a zaɓen 2027 tare da ƴan takararta na shugaban ƙasa da gwamnoni da kuma sauran muƙamai.

A ɓangaren Atiku, a ranar Laraba ya bayyana kamar ba ya ɗaukar yiwuwar fitar ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya daga jam’iyyar adawa da muhimmanci.

Yayin da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, babban mataimaki na musamman ga Atiku kan sadarwar, Phrank Shaibu, ya ce jam’iyyun adawa sun riga sun kammala harkokinsu na cikin gida kuma sun fitar da ƴan takara bisa tsarin kundin mulkinsu da dokar zaɓe ta tanada.

Haka kuma, manyan shugabannin adawa da jam’iyyun siyasa sun nisanta kansu daga ƙudirin fitar da ɗan takara guda ɗaya na shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Jam’iyyun NDC da PRP da LP da AP da wani ɓangare na ADC sun ce ba a cimma irin wannan yarjejeniya ba, yayin da wasu suka dagewa cewa za su fitar da ƴan takararsu da kansu.

Jagoran jam’iyyar NDC, Seriake Dickson, ya karyata tattaunawa kan samun ɗan takarar da kowa ya yarda da shi bayan jam’iyyar ta sanar da tikitin haɗin gwiwar tsakanin Obi da Kwankwaso.

Shi ma shugaban jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce jam’iyyun adawa suna ci gaba da haɗa haɗin kai, abin da suke mai da hankali kai tsaye a kai shi ne kawo ƙarshen mulkin APC.

Sai dai jam’iyyar AP yta yi watsi da lamarin haɗa kai na fitar da ɗan takara ɗaya tilo na shugaban ƙasa, tana nisanta kanta daga taron siyasa na Ibadan, inda aka ce wannan shiri ya bayyana.

Ɓangaren jam’iyyar ADC da Nafiu Bala Gombe ke jagoranta ta ce ba ta cikin yunƙurin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya don yin takara da Tinubu a 2027. Jam’iyyar LP ta yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa tana cikin shirin. Sakatare yaɗa labaran jam’iyya, Ken Asogwa, ya ce, “Yanzu haka dai, ba mu cikin tsarin taron Ibadan. Wannan shi ne matsayin jam’iyyarmu a yanzu,” in ji shi.

A da yake mayar da martani, daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi watsi da yiwuwar jam’iyyun adawa su kayar da Tinubu a 2027, ko da sun fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda.

Ibrahim ya ce babu wani takara daga jam’iyyun adawa da aka saka sunansa a shafin INEC da ya mallaki irin halayen Tinubu, yana bayyana tabbacin cewa APC za ta ci gaba da mulki ko da ƴan adawa sun haɗe zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa har ma ƴan adawa sun san cewa gyaran da Tinubu ya yi ya zama dole don ɗorewar ƙasar nan. “Tsoron da ke cikin zukatan mutane saboda sauye-sauyen da aka kawo yanzu ba ya nan, domin suna fara ganin cewa sauye-sauyen sun kasance masu muhimmanci.”

“Ba zai yiwu ƙasar ta tsira ba tare da gabatar da waɗannan gyare-gyaren ba, kuma gyare-gyaren suna fara haifar da sakamako mai kyau. Duk da tsaurin da mutane ke ji, amma suna jurewa,” in ji shi.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara
Labarai

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Bukaci A Yi Kokarin Karfafa Jagorancin Siyasa Da Kirkire-Kirkire A Aikin Zamanantar Da Rundunonin Sojin Kasar Sin

Xi Jinping Ya Bukaci A Yi Kokarin Karfafa Jagorancin Siyasa Da Kirkire-Kirkire A Aikin Zamanantar Da Rundunonin Sojin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.