Tare da sallama, ina yi wa ‘yan’uwana mata fatan ana ci gaba da aikace-aikacen gida da tarbiyyar yara, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan, Allah Ya nuna mana karshenta lafiya, Ya sanya mu daga cikin wadanda za a ‘yanta amin summa amin.
Idan za a iya tunawa mun tsaya inda muka kawo dan abin da ya shafi ‘Namijin Dare’. Abin da ake nufi da ‘Namijin Dare’ kamar yadda na bayyana a makwannin baya shi ne, yayin da a wasu lokutan a ke samun Aljani ya auri mace, har ma idan aka rashin sa’a yake hana ta samun ciki. Kuma muddin tana tare da shi, ba za ta taba haihuwa ba. Duk da ni ba masani ba ne kan harkar aljanu ba, amma bisa nazarin da na gudanar gami da tuntubar masana, sun tabbatar da cewa alamomin kamuwa da NAMIJIN DARE da mata kadai ke yi su ne kamar haka: Mafarkin jarirai, mafarkin wani na saduwa dake, bacin rai da faduwar gaba a koda yaushe, mafarkin ruwa, yawan ciwon kai, jin motsi a ciki, lalacewar maganar aure ga budurwa, damuwa da rama ko kiba marar misali, da sauran makamanta hakan.
A karshe muka kara jawo hankalin uwargida, ko kuma wadda ta samu kanta cikin irin wannan halin cewa ta gaggauta neman tsarin jikinta, kana ta yawaita addu’o’i da fatan Allah zai ci gaba da kare mu da karewarSa ameen.
A yau kuma za mu dora ne kan abin da ya shafi amfanin dabino wajen kiwon lafiya. Hadisai da ingantattun bayanan tarihi sun bayyana yadda Manzon Tsira (SAW) yake fadin alherin da ke tattare da dabino. Sau tari, ya kan fifita dabino, madara da zuma kan sauran abinciccikan yau da kullum. A matsayinsa na likitan likitoci, Manzo (SAW) ya fi kowa kaifin basirar sanin abin da jikin dan adam yake bukata.
Wasu daga cikin amfanin Dabinon har wa yau sun hada da:
– Yana Sanya kuzari yayin ibadar aure (tsakanin mata da miji)
– Yana taimakawa wajen karin jini
– Yana taimakawa ma’aurata domin kara inganta lafiyarsu.
– Yana Maganin Basir mai sa tsugunni a bayi.
– Yana kara kaifin idanu da lafiyarsa.
– Yana Rage nauyin kiba ko katon tumbi, wanda aka fi sani da ‘Teba.’
– Yana Saurin saukar da hawan jini
– Yana taimakawa kwakwalwa wajen samun basira.
– Yana kariya daga Sihiri.
– Yana taimakawa Mata masu ciki don samun sauki wajen haihuwa.
– Yana kariya daga Sihiri.
- Ko Dabino Na Maganin Ciwon Nono Ga Mata?
Kwarai kuwa, dabino sinadari ne na musamman don warkar da dukkanin cututtukan da mace za ta gamu da su, ko na bayan haihuwa da sauransu.
Yadda za a yi amfani da shi wajen warkar da ciwon nono ga wadda ta haihu kuwa shi ne a rika cin kwayar dabino guda bakwai, asha man tafarnuwa karamin cokali sau daya a rana har na tsawon kwanaki uku.
- Domin Samun Ni’ima Ga Ma’aurata
Ana daka dabino a zuba cikin madara ‘Freesh milk’ sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin lokacin saduwa.
- Samun Kuzari:
Ana cin dabino guda uku, a sha zuma Cokali daya da safe da yamma.
- Yadda Dabino Ke Gyara Fatar Jikin Mutum:
Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska, awa daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan yana saurin gyara fuska. Bincike ya nuna yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon daji (wato ‘Cancer’) ko wacce iri. Haka Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ‘Dabinon Ajuwa yana maganin dukkan cututtuka, kuma duk ranar da mutum ya ci irin wannan dabino na Ajuwa (wato wanda ake tsinkowa daga birnin Madina, wanda aka tabbatar a gonarsa ake samun dabinon), babu wata cuta da za ta same ka a wannan rana ko sammu ko sihiri.’
Tare da