Connect with us

Madubin Rayuwa

Sana’o’in Gargajiya: Wane Hali Fatauci, Kira, Saka Da Jima Ke Ciki?  

Published

on

Cigaba Daga Makon Da Ya Gabata

Fatauci, tun kafin wannan zamani da ake ciki, Hausawa suna da irin nasu tsari wajen tafiyar da harkokin kasuwanci. Wannan tsari ana iya dubansa ta fuskoki kamar: kasuwancin cikin gida da kuma na waje. A cikin gida akwai kasuwanni na garuruwa wadanda ake tafiyar da harkokin kasuwanci ta hanyar tafiye-tafiye. A irin wannan kasuwanci ana musayar abubuwan sayarwa ne, misali manomi ya ba masaki kayan gona don ya karbi kayan saka, ko ya ba makiyayi don ya amshi wata dabba da sauransu. An dade ana yin irin wannan tsari na cinikayya a kasar Hausa har zuwa cikin karni na goma sha takwas da aka shigo ta hanyar yin amfani da kudin wuri da biringizau don yin saye da sayarwa a duk fadin Afirka ta yamma(Nadama, 1977:138).

Idan mun duba za mu ga cewa, har yanzu akwai wannan dadaddiyar sana’a amma hanyar gudanar da ita sun bambanta. Domin a da a Jakuna da rakuma da dawaki ake amfani wajen tafiye-tafiye da kuma daukar kaya. Sannan Madugu ko Maduga suke jagorantar Fataken.

Kira, yana da matukar wuya a ce ga lokacin da Bahaushe ya fara narka tama ya mayar da ita karfe don yin amfanin yau da kullum da shi, amma duk da haka nan an dan sami haske wanda ya bayyana cewa Hausawa sun kware wajen narka tama da mayar da ita karfe wanda ake sarrafawa zuwa abubuwan amfanin gida da makamai da kayayyakin aikin gona da na kwalliya. Kira sana’a ce wadda aka fi yi a lokacin rani domin tanadar kayan aikin noma, amma duk da haka ana yin ta a kowane lokaci na shekara domin samar da kayan amfanin gida na yau da kullum. Makera sun kasu zuwa gida biyu, akwai makeran baki da makeran fari. Makeran baki su ne suke tono tama su narka ta don ta zama karfe wanda suke yi sun hada da fartanya da masassabi da gatari da lauje da sungumi da adda da dai sauransu domin yin ayyukan gona. Haka kuma makeran baki suna kera takubba da gariyo da tsitaka da masu da kibau da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen yin ayyukan cikin gida na yau da kullum. Haka kuma su ne suke samar da kayan aikin wanzanci wadanda suka hada da asake domin yin aski da kaciya da kuma kalaba wadda ake amfani da ita wajen cire belun-wuya. Suna kuma yin askar tsaga wadda ake amfani da ita wajen cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta magani da ta kwalliya da sauransu. (Bashir, 2012:484)

Saka, sana’a ce wadda ake sassarka zare ko bawo ko kaba don a mayar da su wani abu mai fadi kamar tufafi ko shimfida. Ana amfani da zaren auduga ne wanda mata suke kadawa domin sakar tufafi. Masaka wato masana’antar da ake sarrafa zare domin yin suttura ita ma ta kasu gida biyu. Akwai masakar tsaye wadda mafiyawanci mata ne suke amfani da ita don yin sakar gwado ko zanen kujera ko dan goyo wanda ake goya jarirai. Akwai kuma masakar zaune wadda maza ne suka fi yin amfani da ita wajen yin sakar sauran abubuwa.

Hakika wannan sana’a tana da matukar mahimmanci a kasar Hausa domin kuwa ba domin ita ba da an rika tafiya tsirara. Wannan a fili yake, suttura ita ce alamar da take bayyana bambanci a tsakanin mutum da dabba. A cikin mutane ma da suttura ake iya rarrabe bambancin al’adu. Masana’atar saka ta taimaka sosai wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Hausa. Wannan kuma ya samu ne sakamakon kayayyakin da ta rika samarwa wadanda ake sayarwa a kasuwannin cikin gida da na kasashe makwabta (Alhassan 1982:54).

Amma saboda makirci da zagon kasa irin ta Turawan mulkin mallaka a yau sana’ar saka ma ta sume tana neman mutuwa ko kuma a ce bacewa daga kasar Hausa saboda shigowar sutturu da Turawa suka rinka yi, sannan ‘yan kasuwarmu da mahukuntanmu da al’ummar kasa suka tafi a kan hakan.

Jima, sana’a ce wadda ake sullube fata don a fitar da gashin da yake jikinta. A irin wannan masama’anta da ake kira majema ana sauya fata daga halinta na asali na gashi da kaushi a sarrafa ta, a gyara ta yadda za ta yi laushi kamar suttura wadda a wancan zamani ake kiran ta Maroco.

Bayan an gyara fata ta yi kyau ana sayar da ita ga dukawa, kuma mafi yawancin fatar da aka gyara tana daga cikin manyan muhimman hajoji da ake safararsu daga kasar Hausa zuwa kasashe makwabta na kusa da na nesa.

Sana’ar jima ta samu sauyi ta hanyar aiwatar da ita domin a halin yanzu mafiya yawancin masu yin ta suna amfani da sinadarai da ake kawowa daga kasashen Turawa.  Wadannan sinadarai suna rage warin wannan fata. A takaice suna saukaka yin wannan sana’ a ta jima ta hanyoyi da dama.

             Za mu dora sati mai zuwa.

 
Advertisement

labarai