Muazu Hardawa" />

Sanata Nazif Ya Sama Wa Mutane 250 Aiki Tare Da Duba Lafiyar 6,000 Kyauta  -Galadima Itas

Children ward at the General Hospital in Calabar.

A ci gaba da kokarin sa na ganin ya tallafawa mutanen shiyyar Katagum da ayyukan yi tare da ingantacciyar lafiya, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa a majalisar dattijan Nijeriya Injiniya Sulaiman Nazif Gamawa ya samawa mutane 250 ayyukan yi wanda ya shafi shiga ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma shiga shirye shiryen samar da ayyuka na gwamnatin tarayya a karkashin shirin koyon sana’a. Har way au kuma ya kawo likitoci sun duba lafiyar sama da mutane dubu shida inda aka musu gwadi tare da basu magunguna da aikin fida kyauta.

Alhaji Galadima Abba Itas mai tallafawa Sanata Nazif Gamawa a harkokin siyasa shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilin mu a Bauchi ta wayar tarho.  Inda ya bayyana cewa kowane mako Sanatan yana zuwa wasu daga cikin kananan hukumomi bakwai na shiyyar Katagum domin tallafawa jama’a saboda ganin irin mawuyacin halain da mutane suka shiga na rashin ayyukan yi a wannan lokaci, don haka ya ke raba kayan koyon sana’a ga matasa da kuma mata don su samu hanyoyin dogara da kan su.

Don haka ya ce a halin yanzu dubban mutane sun amfana da wannan shiri na bayar da jari da kayan koyon sana’a da kuma duba lafiya a kananan hukumomin Katagum da Gamawa da Shira da Giyade da Jama’are da Itas Gadau da Zaki.

Galadima Abbba ya kara da cewa amma shirin samar da aiki na gwamnatin tarayya, ya zuwa wannan lokacin Sanata Nazify a samawa sama da mutane 100 aiki a hukumomin gwamnatin tarayya, yayin kuma da ya samawa mutane 150 ayyukan koyon sana’a wanda gwamnatin tarayya ta fito da shi don ganin an tallafawa matasa wadanda suka yi karatu da wanda ba su yi karatu ba.

Don haka a wannan waje ya samawa mutane 150 aiki yadda aka samu jimlar mutane 250 a karkashin wannan shiri na aikin dindindin da kuma aikin koyon sana’a wanda shima gwamnatin tarayya ta fito da shi kamar aikin gwamnati. Kuma wannan sana’a ta kunshi sarrafa na’ura mai kwakwalwa da gyara hasken lantarki mai aiki da rana da kuma gyaran rijiyoyin burtsatse da tonon su da sauran ayyukan zamani da ake iya dogara da su a matsayin sana’a mai kawo arziki da wuri.

Bayan haka Sanata Sulaiman nazif ya dauki nauyin dalibai da basu kudin karatu a makarantu da dama na kasar nan tare kuma da bayar da tallafin karatu wanda ya kunshi dalibai a dukkan gundumomi 116 da ke shiyyar Sanatan Bauchi ta arewa.

Yayin da kuma akwai wasu dalibai da ke karatu a kasashen ketare amma suka samu matsalar kudin tallafi daga hukumomin da ke tallafa musu inda suma ya agaza musu da kudin fam na ingila da kuma dala don ganin wannan karatu nasu bai lalace ba.

Galadima Abba Itas ya kara da cewa Sanata Sulaiman Nazif a kullum na nuna damuwa game da rashin aiki da matasa ke fama da shi, amma kasancewar mutanen yankin Bauchi ta arewa sun dogara da nomar rani, saboda haka ya sayi injinan bayi don rabawa matasa da suka taimaka wajen shiga harkar aikin gona da kuma wadanda suka tallafawa tafiyar siyasar wannan gwamnati, inda a kowace karamar hukuma ya bayar da tallafin kudi wanda ya kama daga milyan  biyu zuwa milyan uku don agazawa mutanen da ke cikin wahala ko suke da bukatar tallafi.

Saboda haka ya bayyana cewa sun yi haka ne don ganin kowa ya samu abin da zai tallafi kansa a matsayin jarin da zai sa cikin harkar sat a kasuwa saboda mutane su daina daukar yawon siyasa a matsayin sana’a.

Bayan haka kuma sanatan ya bayar da aikin gyaran masallatan da suka lalace da kuma gina wasu sabbi don ganin  mutane sun daina sallah a cikin masallatan da suke zubar da ruwa ko basu da gyara musamman ganin yadda ake fiskantar damina a daidai wannan lokaci.  Inda ya kara da cewa bayan wuraren ibada Sanatan ya samar da asibitoci bakwai a kowace karamar hukuma da ya ke wakilta domin amfanin jama’ar yankin.

Bayan haka kuma ya bayar da gina wasu kananan asibitocin sha katafi da gyara asibitocin gwamnati da suka lalace.

Game da lafiyar jama’a kuma Sanata Sulaiman Nazif ya samar da likitocin musamman inda suka zo cibiyar kiwon lafiya da ke garin Azare suka duba sama da mutane 6000 aka kuma basu magungunan da suke bukata kyauta yayin da kuma aka yi wa sama da mutane 200 aikin tiyata kyauta don samun lafiya saboda wasu sun jima suna fama da matsalolin cututtuka amma basu da halin a yi musu aiki.

Don haka ya kawo likitocin suka duba mutane kyauta kuma suka yi musu dukkan aune aunen da suka dace kyauta. Yayin da a gefe daya masu fama da larurar ido suma an duba mutane da dama kuma an basu gilasai wasu an basu magani wasu kuma an musu aiki kyauta don su samu gudanar da hidimomin su na rayuwa kamar yadda kowa ke gani.

 

Exit mobile version