Sanatan Barau Jibrin Ya Raba Shanun Noma A Kananan Hukumomin Kunchi Da Rimin Gado

Daga Abdullahi Muhannad Sheka, Kano

A Ranar Talata 30 ga watan June Shekara ta 2021 Sanatan Kano ya Arewa Barau I. Jibrin ya kaddamar rabon Shanu Ga Manoma Da Makiyaya na yankin Kano Ta Arewa ga al’ummarsa, Kamar yadda mai magana da yawun Sanatan Honarabul Alhaji Shitu Madawaki kunchi, Wanda ya Jagoranci Tawagar Sanatan wajen kaddamar rabon Shanun, da aka fara da kananun Hukumomin Rimin Gado Da Kunchi, Wanda kowacce karamar Hukuma ta amfana Da ahanun Noma guda ashirin Da Takwas (28), ya Shaidawa LEADERSHIP A Yau Juma’a.
Akalla kimanin Shanu dari uku da sittin da hudu (364) me aka tsara za’a raba a yankin kananan Hukumomin Kano ta arewa, kananan Hukumomin da Sanatan Yake Wakilta A Zauren Majalissar Dattawan Nigerian, Kowacce karamar Hukuma zata amfana Da Shanu ashirin da takwas (28).
Da take tsokaci Kan wannan kabakin arzikin da Wakilin al’ummar Kano ta arewa ke Saukewa al’ummar sa, tsohon shugaban karamar Hukumar kunchi Honarabul Dr. dallami Zakari Unguwar Gyartai, ya bayyana cewa, duk dadewar da ya yi a duniya da shiga sabgar siyasa Da ya yi, bai taba ganin mutum mai son cigaban yankinsa da al’ummarsa irin Sanata Barau I Jibrin ba.
Ya ci gaba da cewa, akalla a iyaka karamar Hukumar kunchi kawai sai da ya lissafta manyan ayyuka kimanin Guda 15 wanda Sanatan ya yi a wannan karamar Hukuma, Ya kara da cewa, Ya yi Imani dukkanin kananan Hukumomin da Sanatan ke wakilta haka yake masu lugudwn irin wadannan ayyukan alhairi.
Shima anasa jawabin tsohon shugaban kkaramar Hukumar Rimin Gado, Honarabul Alhaji Garba Shu’aibu Rimin Gado ya bayyana Cewa, sun rasa da wane baki zasu godewa m Sanata, ya ci gaba da Cewa, dukkanin waau Kokensu a yanzu ahi ne ke share masu hawaye.

Exit mobile version