Mambobin Kwamitin Ba da Lamuni na Jama’a na Majalisar Dattawa sun nuna rashin gamsuwarsu ga wasu jami’an Ma’aikatar Tsaro da suka biya Naira 968.8m ga ’yan kwangila ba tare da amincewa ba. Rahoton na Babban jami’in binciken kudi na Tarayya, ya nuna wa ma’aikatan musamman biyan makudan kudade ga ’yan kwangilar. An yi shi ne don samarwa da kuma bayar da lambobin yabo don bikin tunawa da ranar samun ‘yancin kan Sojoji, amma ana zargin ba tare da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya da kuma Kwamitin bayar da kwangila na Minista ba.
Rahoton na AuGF ya tuhumi jami’an ma’aikatar tsaro da saukaka biyan kwangilolin duk da rashin amincewar da Mataimakin Darakta (Kasafin Kudi) ya gabatar a cikin wata takarda mai kwanan wata 24 ga Afrilu, 2013.
Shugaban SPAC, Sanata Matthew Urhoghide, ya ci gaba da tambayar babban mai binciken saboda jami’an ma’aikatar tsaron sun kasa girmama gayyatar kwamitin don su bayyana bangarensu na zargin. Urhoghide ya lura da matukar damuwa cewa an gabatar da jerin gayyata ga ma’aikatar ba tare da wata amsa ba. Ya ce, saboda haka kwamitin ba shi da wata mafita face ya ci gaba da tambayar. AuGF ya ce an bayar da kwangilar ne a shekarar 2010, kuma an biya kashi 50 na kudin kwangilar ga ‘yan kwangilar yayin da aka biya ragowar kudin a ranar 26 ga Janairun 2015 ga dan kwangilar.
“An bayar da kwangilar samarwa da kuma bayar da lambobin yabo da kinti ribbons don bikin cikar ranar samun ‘yancin kan Sojojin Nijeriya a kan jimlar kwangilar da ta kai Naira miliyan 968,830,000.00. An biya duka kudin kwantiragin a watan Janairu. An biya Naira miliyan 484,415,000.00 a shekara ta 2010 wanda ke wakiltar kashi 50 cikin 100 na kwangilar kuma an biya ragowar Naira milyan 484,415,000.00 a ranar 26/01/2015 baitul malin kuɗi na lamba 4001.