Maigari Abdulrahman" />

Sarkin Patigi Alhaji Ibrahim Chatta Umar Ya Rasu

Sarkin garin Patigi na karamar hukumar mulkin ta Patigi da ke jihar Kwara, Alhaji Ibrahimm Chatta Umar, ya rasu.
Alhaji Umar ya rasu na a wata Asibiti da ke Abuja a daren Talata bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya, labarin rasuwarsa ya fito ne daga magatakardan sarkin Ilorin, Muritala Raheem.
Kafin rasuwarsa, Alhaji Chatta shi ne mataimakin majalisar sarakuna ta jihar. An bizne mamacin ranar Laraba a garin na Patigi, da misalign karfe 2 na rana.
A wani labarin kuwa, sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya bayyana alhininsa na rashin mamacin basaraken, ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai mutunci da girmama jama’a, sarkin y ace, rashin sa babban rashi ne ga al’ummar jihar bakidaya.
A cikin takardar sakon ta’aziya da sarkin ya fitar ta hannun sakataren gidauniyar zaman kafiya da ci gaba ta masarautar, Mallam Abdul’aziz Arowona ya bayyana cewa, mamacin babban alamin zaman lafiya ne da hadin kai a cikin daukacin Nupawa da ke Kwara da sauran wurare daban.
Mutuwarsa babban gibi ne da za a dade ba a cike gubin ba, kuma ba a manta shi ba kurkusa. Muna rokon Allah da yafe kurakuransa, ya sanya shi a aljannar faddausi, Allah ya ba wa iyalan mamacin hakurin rashi, inji Etsa Chatta Umar.

Exit mobile version