Rabiu Ali Indabawa" />

Saudiya Ta Karu A Cikin Masu Zargin Iran Da Kaiwa Tankokin Mai Hari

Yarima mai jiran gado a Saudi Arabiya ya zargi Kasar Iran da kai hare-hare a kan jiragen dakon mai a kan tekun Oman, kana ya yi kira ga Kasashen duniya su dau kwakkwaran mataki a kan wannan batu.

Abubuwan fashewa da suka lalata jiragen Norway wanda kamfanin Front Altair ke mallaka da kuma na kamfanin Kasar Japan Kokuka Courageous ya faru ne a ranar Alhamis yayin da Firai ministan Japan Shinzo Abe yake wata ziyara a Tehran domin shiga tsakani a kan karin tankiya tsakanin Amurka da Iran.

Wata jaridar gwamnatin Saudi Arabia, ta rawaito kalaman yarima Mohammed Bin Salman, a wata hira da ya yi da manema labarai yana fadin cewa, Iran ba ta mutunta ziyarar da Firai ministan Japan ke yi a Kasarta ba, ta mayar masa da martani da kai hare-hare a kan jirage biyu ciki har da na Kasarsa Japan.

Iran da ta musunta wannan zargin tana da hannu a wadannan hare-hare, ta baiwa jakadar Birtaniya a Tehran sammaci a jiya Asabar bayan Birtaniya ta yiwa Kasar zargin kai hare-haren, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Iran na ISNA.

A wannan zaman tare da jami’an ma’aikatar harkokin waje, Iran ta caccaki Birtaniya da kakkausan lafazi, kuma ta ce ba za ta lamunta da matsayar Birtaniya a kan batun hare-haren tekun Oman.

Exit mobile version