Shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani na babban birnin Tarayya Abuja Gwani Muhammad Zangina ya jinjinawa Majalisar mahaddata Alkur’ani bisa karramawar da ta nuna wajen aika babbar tawaga karkashin Jagorancin Sakataren Majalisar na kasa Goni Sanusi Abubakar inda suka halarci daurin aure da Saukar Karatun ‘yayan Gwani Zangina Wanda aka gudanar ranar Asabar a Kano.
Gwani Zangina yace irin zumunci shi aka San halin Alkur’ani dashi, Kuma akansa muke har yanzu. Don Haka sai ya bukaci ‘yan uwa da kara jajircewa wajen gudanar da addu’o’i bisa halin da makarantun Allo suka tsinci Kai a Ciki, Gwani Zangina ya jawo ayoyi da hadisan Annabi domin hakurkurtar da ‘yan uwa bisa irin barazanar da wasu ke yiwa harkar makarantun tsangaya Wanda yace wannan duk lokacin ne.
Gwani Zangina ya godewa ‘yan uwa wadanda suka samu sukunin halartar wannan taro, dama wadanda addu’o’i suka Aiko duk muna godiya, a karshe ya yi fatan kowa ya koma gidansa lafiya.
Goni Sunusi Abubakar Wanda ya wakilci Shugaban Majalisar mahaddata Alkur’ani na kasa Gwani Aliyu Saluhu Turaki ya bayyana cewa shugaban yaso kasancewa a wannan wuri domin ya san ahalullahi zasu hallara, Amma saboda abububawan da suka taru yasa Bai samu halartar wiring wannan Sauka ba, Amma zuciyarsa na tare damu a wannan wuri.
Goni Sunusi Abubakar ya isar da sakon shugaban na bukatar matsawa da addu’o’i domin fatan Allah ya Kawowa wannan kasa tamu karshen matsalolin taro da matsin tattalin arziki da ake fuskanta.
Shi ma mataimakin Shugaban Majalisar mahaddata Alkur’ani shiyyar Abuja Gwani Abdurrazak ya bayyana farin cikinsa bisa baiwar samun Alkur’ani da wadannan Yara biyar suka you, sannan ya yi addu’ar fatan samun zaman lafiya a auren da aka daura.