Sayayyar Da Aka Yi A Ranar 12 Ga Disamba Ta Taimaka Wajen Karuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin

A lokacin da ake kusa da karshen shekarar bana, sayayyar da aka yi a ranar 12 ga watan Disamba, wato bikin sayayya daban da a kan yi a shafukan Intanet ban da wanda aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a nan kasar Sin, ta sake bayyana yadda Sinawa suke kashe kudi suke sayen kayayyakin da suke bukata. Masana sun bayyana cewa, irin wannan tattalin arziki da ake yi a kan shafin intanet ya samarwa masu sayayya sabuwar dama a lokacin da har yanzu ake tinkarar annobar COVID-19. Sun yi hasashen cewa, sayayyar da za a yi ta kafofin shafin intanet za ta samu karuwa matuka a badi. Yanzu ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

“Na sayi wasu jan baki da tawul da wasu kayayyakin masarufi. Na kan sayi abubuwan da nake bukata a kafar bidiyo da ake watsawa kai tsaye saboda farashin kaya a ciki yana da rahusa. Bugu da kari, har yanzu ana cikin yanayin tinkarar annobar, ba na son fita waje. Babu matsala idan muka sayi kayayyaki daga shafukan intanet.”
“Na kwatanta farashin kayayyaki, kamar tukunya da man girki na Oliver da ake amfani da su a gida, da na tabarau da nake bukata da ake sayarwa a ranar 12 ga watan Disamba, sun yi araha kwarai da gaske.”
Game da karfin sayayyar Sinawa, Mr. Zhang Jianping, direktan cibiyar nazarin hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin shiyya-shiyya a hukumar nazarin harkokin cinikayya ta ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, yana mai cewa, “Sabo da masana’antu da kamfanoni sun farfado da harkokinsu kamar yadda ake fata a karshen rabin shekarar bana, yanzu harkokin sayayya na kasar Sin ma sun samu farfadowa fiye da kima. Daga rubu’i na uku da na hudu na bana, kasuwanin sayayya suna ta samun karuwa, musamman a cikin watanni biyu da suka gabata, sun samu karuwa sosai.”
Bisa alkaluman da kamfanin Pinduoduo ya bayar, an ce, ’yan mata sun fi son sayen kayayyakin kwalliya a dandalin “GlobalGo” dake shafin intanet na Pinduoduo, sannan injunan wasa da manhajojin wasa da kayayyakin wasan Lego sun fi samun karbuwa. Bugu da kari, kayayyakin gina jiki da magungunan hana zubewar gashi sun kuma samu karuwa cikin sauri fiye da kima.
Dadin dadawa, bisa alkaluman da kamfanin Sunning ya bayar, an ce, sabo da lokacin sanyi ya yi, a ranar 12 ga watan, yawan injunan dumama daki da aka saya ya karu da kashi 426 cikin dari, kamar yawan bargo da aka sayar ya karu da ninki 30, rigunan sanyi da aka sayar sun karu da ninki 7 bisa makamamancin lokacin bara. Bugu da kari, injunan lantarki da ake amfani da su a gida da abubuwan gina jiki suna ci gaba da samun karbuwa. Alal misali, yawan injunan bayan gida na zamani da aka sayar ya karu da ninki 5.5, yawan injunan dumama abinci mai aiki da microwave da aka sayar ya karu da ninki 4.6. Har ma yawan injunan jinya da ake amfani da su a gida da aka sayar a shafin intanet ya karu da ninki 3 bisa makamancin lokacin bara.
Bayan bullar annobar COVID-19 a bana, wasu rumfuna da yawa ba su iya yin kasuwanci kamar yadda ya kamata ba, wannan ya sa an samu damar bunkasa tattalin arziki ta shafin intanet. Farfesa Zhang Jianping ya kara da cewa, “Annobar ta sa an samu damar karfafa aikin sayar da kayayyaki da bunkasa tattalin arziki ta shafukan intanet. A farkon rabin shekarar bana, kasar Sin ta cimma nasarar shawo kan annobar. Sakamakon haka, kamfanonin kasuwanci da kamfanoni masu sufurin kayayyaki na kasar Sin, musamman wadanda suke sayar da kayayyaki a shafukan intanet sun samu damar farfado da harkokinsu kamar yadda ake fata cikin sauri sosai. Masu sayayya ma sun yi tsimin lokaci da yawa wajen sayen kayayyaki a shafukan intanet. Sabo da haka, an gano cewa, sayayyar da ake yi a shafin intanet za ta ci gaba da samun karbuwa cikin sauri. Yawan kayayyakin da za a saya daga shafukan intanet maimakon rumfunan da aka bude a titi zai karu.”
Farfesa Zhang Jianping ya bayyana cewa, badi farkon shekara ce da za a kaddamar da “shirin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na tsawon shekaru biyar na 14”, an yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da farfadowa cikin sauri sosai. (Sanusi Chen)

Exit mobile version