Muhammad Awwal Umar" />

SCONY Ya Tallafawa Kananan ’Yan Kasuwa A Minna

Shugaban karamar hukumar Chanchaga, Hon. Yusuf Inuwa Fuka (Scony) ya sha alwashin tallafa wa kananan ‘yan kasuwa akan shirinsa na farfado da kananan kasuwanci a karamar hukumar. Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bada tallafin naira dubu goma-goma ga masu sana’ar shayi da wanki da guga su kimamin dari biyu da saba’in da biyar.

Shugaban ya ce gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin bunkasa kananan kasuwanci ta yadda kudade zasu samu damar walwala a cikin al’umma, akan haka suka ga dacewar su fara da matasa da mata da kuma masu kananan kasuwanci da masu sana’ar hannu. Yau mun zakulo masu sana’ar shayi da wanki da guga a sassan mazabun da ke karamar hukumar nan dan farawa da naira miliyan biyu da dubu dari bakwai da hamsin, zamu sanya ido sosai dan ganin ba mu tsaya nan ba, kowa yasan halan da ‘yan kasuwa ke ciki yanzu, zamu mayar da hankali akan wannan shirin na inganta kananan sana’o’in hannu a karamar hukumar nan, domin irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Da yake karin haske ga wakilin mu, babban darakta mai kula da walwala da samarwa matasa aikin yi ta jihar Neja, Hon. Muhammed Nma Kolo ya ce wannan shirin abin a yaba ne domin kusan ire-iren wadannan shurarakun sune gwamnatin jiha ke jawo hankalin kananan hukumomi da yi domin bunkasa kananan sana’o’in hannu a cikin al’umma.

Dan haka a matakin jiha zamu ga inda ya kamata mu shigo dan tallafaw ita karamar hukuma, lallai na yaba da kudurin mai girma shugaban karamar hukuma Hon. Yusuf Inuwa Fuka, domin wannan kudurin jam’iyyar APC, samar da walwala da inganta tattalin arzikin kasa, taimakawa kananan ‘yan kasuwa shi ke kawo habbakar tattalin arziki a cikin al’umma.

Hon. Yakubu Sallau, tsohon shugaban karamar hukumar ta Chanchaga, ya yabawa shugaban mai ci, ya ce lallai ya bar baya mai anfani a karamar hukumar nan, irin wannan shirin shi mu ke yi tun farko, yau shugaba mai ci kuma ya dora a inda muka tsaya, lallai a matsayin mu na masu kishin karamar hukumar nan zamu ci gaba da na shi goyon baya dan samun nasarar karamar hukumar Chanchaga gaba daya.

Da yake karin haske, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar ta Chanchaga, Alhaji Khalid Hassan, ya ce wannan aikin na daga cikin muradun jam’iyyarsu ta APC na farfado da kananan kasuwanci ta hanyar bada tallafi. Ya ci gaba da cewar yanzu shiri yayi nisa na biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai ‘yan asalin karamar hukumar Chanchaga, bayan nan a jam’iyya ce da kwarin karamar hukumar zamu kara tashi haikan ga dukkanin hukumomin gwamnati ta yadda za a inganta rayuwar ‘yayan marasa karfi.

Burin APC tallafawa marasa karfi, tallafawa masu rauni, APC a karamar hukumar Chanchaga da goyon bayan nagartattun ‘yayanta sai ta tauraruwa a gidan kowa za a yi alfahari da ita.

Da dama daga cikin wadanda suka samu tallafin sun yabawa kudurin shugaban karamar hukumar musamman na ganin ya ceto kananan kasuwanci daga durkushewa.

Tsoffin shugabannin karamar hukumar ta Chanchaga, da shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa na daga cikin wadanda suka halarci bukin tallafin. Kungiyar turaku ta tsira da tallafin dubu dari biyar don inganta muradun kungiyar.

 

Exit mobile version