Shahararren Malamin nan kuma dan Nijeriya Sheikh Ahmed Lemu ya riga mu gidan gaskiya, rahoton jaridar LEADERSHIP.
A cewar wani sakon da diyar sa, Maryam Lemu ta wallafa a Facebook, malamin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a Minna.
An haifi Shaikh Ahmed Lemu a unguwar Lemu, Jihar Neja, a ranar 21 ga Disamba, 1929. Ya fara karatun sa na farko a Makarantar Al-Qur’ani a 1932, sannan ya yi makarantar firamare (1939), sannan kuma makarantar sakandare duk a unguwar Lemu. , daga nan ne ya sami takardar shedar kammala makarantar sakandare a 1948.
Bayan haka, ya shiga Makarantar Shari’a (Makarantar Nazarin Larabci) a Lemu inda ya sami Takardar shedar kammala makarantar, matakin farko (1950) da na biyu (1952) a cikin Harshen Larabci, Nazarin Addinin Musulunci, Shari’a da Ilimin bai daya. A 1954, ya tafi Ingila don yin karatu a Jami’ar London bangaren Makarantar Nazarin Afirka.
Ya sami shaidar kammala Babban Ilimi (Advanced Level) a bangaren Tarihi, Larabci, Hausa da Harsunan Farisanci a 1961, sannan kuma ya samu shaidar digiri a Nazarin Afirka a 1964.
Dakta Shaikh Ahmed Lemu ya yi aiki a fagen ilimi sama da rabin karni, a lokacin ya gudanar da ayyuka daban-daban na koyar da ilimi. Ya fara ne a matsayin malamin koyar da harshen larabci, harshen turanci da karatun addinin musulunci a makarantar sakandaren gwamnati da ke Bida tsakanin 1953-1960. A shekarar 1960, ya zama babban malamin koyar da harshen larabci, da karatun addinin Musulunci da Ilimi, sannan kuma mai kulawa a Makarantar Koyon Larabci da ke Kano, sannan ya zama Daraktan makarantar sannan kuma Mataimakin Daraktan Ilimin Sakandare na Gwamnati a 1965.
Ya zama Shugaban Kwalejin Koyar da Malamai ta Arabiyya a 1966, Babban mai kula da bangaren karantarwa a 1970 kuma Babban mai kula da bangaren karantarwa ta Jihar Sokoto a 1971 – 1973. Ya kuma yi aiki a matsayin Daraktan Fasaha (1974-1975) da Daraktan Ilimi da tsare tsare (1975-1976) a Jihar. A shekarar 2009, an nada shi mai ba da shawara a Jami’ar Fountain da ke Osogbo, Nijeriya.
Dr. Shaikh Ahmed Lemu sanannen malamin addinin musulunci ne, wanda yayi shuhura a tsakanin Musulmin Yammacin Afirka kuma ya samu daukaka da girmama acikin duniyar musulunci. Ya kasance hamshakin mai ilimi, Musulmi mai kishin addini kuma mai kira ga adalci ga jama’a matsakaita Ya kuma kasance mai matukar goyon bayan ‘yancin mata.