Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Sharhin Laliga: Wa Ta Gangano?

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in WASANNI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abba Ibrahim Wada

A duk shekara kusan za mu iya cewa kungiyoyi biyu ne su ke mamaye gasar Laliga ta kasar Spaniya, sai dai a shekarun baya kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta shiga tsakanin wadannan manyan kungiyoyi inda ta lashe gasar ta Laliga a karon farko cikin shekaru  sama da ashirin inda ta lashe gasar a shekara ta 2014.

samndaads

Kungiyoyi  9 ne dai su ka taba lashe gasar a tarihi, inda kulob din Real  Madrid ne ya fi lashe gasar wanda ya lashe har sau 33 yayin da Barcelona ta lashe gasar sau 24, sai Atletico Madrid wadda ta lashe gasar sau 10.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce ta ke kare kambu a wannan shekarar bayan da ta lashe gasar a kakar wasan da ta gabata.

Kulob din Barcelona shi ne kusan ya mamaye shafukan jaridu a cikin watan Agusta sakamakon siyar da shahararren dan wasan kungiyar, Neymar JNR. Hakan ya sa masana su ke ganin kamar kungiyar ba za ta tabuka komai ba ganin kuma duk da ta siyar da dan was an, amma ba ta mayar da gurbinsa da wani babban dan wasan ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce dai a halin yanzu ta ke jan ragamar Laliga bayan da ta buga wasanni biyar kuma duk ta na samun nasara a kai, sai dai Real Madrid da a ke ganin kamar ita za ta buga abin a zo a ga in sakamakon yawan kwararrun ’yan wasanta da kuma a yanzu ta na kan ganiyarta sai ga shi ta buga wasanni biyar ta yi canjaras a guda uku duk a gida yayin da ta lashe wasanni biyu kawai na waje, sannan ta fadi wasa guda.

Amma ko mene ne ya jawowa Real Madrid din wannan koma baya?

Real Madrid ba ta yi wani abin a zo a gani ba a kasuwar siyan ’yan wasa ta bana sakamakon sanin da a ka yiwa kungiyar da siyan manyan ’yan wasa, sai ta bige da siyan matasan ’yan kwallo.

Wannan ba sabon abu ba ne. Kowa ya san yadda Zidane ya nuna sha’awarsa a fili wajen son dan wasan Chelsea, Edin Hazard, inda tun kafin ya zama kociyan Real Madrid an san Zidane wajen yabon wannan dan wasa a lokuta daban-daban.

Hakan ya sa a ke tunanin kungiyar za ta neme shi a wannan kakar ganin yadda dan wasan shi ma ya nuna sha’awarsa ta komawa kungiyar kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Sai dai dan wasan ya samu ciwo har a ka yi ma sa tiyata a kafarsa wanda wannan kusan ya na daya daga cikin dalilin da ya sa kungiyar ta hakura da dan wasan, sai dai kuma a waje daya ita ma Chelsea ba ta da niyyar siyar da dan wasan sakamakon ita ce ta lashe gasar Firimiya ta kasar Ingila wanda hakan ya na nufin ita ma za ta fafata a gasar zakarun Turai ta wannan shekarar.

Kylian Mbappe dai shahararren dan wasa ne a duniya dan shekara 18, wanda tauraruwarsa ta haska a kakar wasan da ta gabata, kuma dan wasan an danganta shi da komawa  kungiyar ta Real Madrid.

Dan wasan wanda dan kasar Faransa ne shi ma Zidane ya nuna sha’awarsa ta komawa kungiyar karara yayin da kungiyar ita ma ta nuna sha’awarta na daukar dan wasan sai dai dan wasan ya yi tsada sakamakon kudin da kungiyarsa ta Monaco ta saka ma sa kusan za mu ce ya yi yawa.

Sai dai kuma Real Madrid ta na bukatar dan wasan gaba ganin yadda a yanzu shekaru sun yiwa dan wasan gaba na kungiyar yawa, wato Bwnzema.

An yi tunanin kungiyar idan ta siyar da Morata wanda ya koma kungiyar Chelsea za ta yi amfani da kudin domin siyo Mbappe duk da cewa sai kungiyar ta cika kudi sosai.

Sai dai daga baya rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta bayyana cewa dan wasan  ya yi tsada, saboda haka ba za ta iya biyan kudin da Monaco ta ke bukata ba.

Kusan an ce ra’ayin Zidane da Perez, shugaban Madrid, ya zo daya wajen fara tunanin siyan kananan ’yan wasa, ba kamar yadda kungiyar ta ke yi a baya ba na siyan shahararrun ’yan wasa. Wannan ya samo asali ne bayan da kungiyar ta ga matasan ’yan wasan kungiyar a yanzu su na buga abin a zo a gani; hakan ya sa su ka fara canja tunani.

Duk da cewa kungiyar ta so siyan Hazard da Mbappe, amma ba ta samu ba, sai dai za mu iya cewa ai indai magana a ke yi ta kudi, to kungiyar ba ta da matsala idan mu ka duba tarihi a baya mu ka ga irin yadda kungiyar ta kashe kudin wajen siyan manyan ’yan wasa irinsu shi kansa kociyan kungiyar na yanzu, wato Zidane da Cristiano Ronaldo da Kaka da Benzema da sauransu.

A lokuta da dama musamman a kakar wasan da ta gabata idan wasa ya kwacewa Zidane ya kan yi amfani da James da Morata kuma ya kan samu nasara.

Akwai wasannin da kungiyar ta ke samun kanta cikin kunci, ’yan wasa irinsu Ronaldo Bale da Benzema duk da cewa su na cikin wasan amma su kasa zura kwallo a raga, daga baya kuma Zidane ya yi amfani da Morata da James kuma ya samu nasara. Wannan abin ya faru sau da dama a kakar wasan da ta gabata.

Sai dai kungiyar ta siyar da Morata sannan ta bayar da James a matsayin aro ba tare da ta maye gurbinsu ba, wanda a na ganin wannan babban kuskure ne kungiyar ta yi.

Zan iya cewa an bayar da aron James ne domin Asensio yasamu damar buga wasanni sosai, wanda hakan kuskure ne, saboda wasannin da kungiyar za ta bawa dan wasan a wannan kakar za su yi yawan da zai yi saurin gajiya.

Akwai matsaloli da dama a kungiyar a yanzu wanda hukumomin kungiyar da shi kansa kociyan kungiyar suna bukatar zama a teburin shawara don ganin sun saisaita al’amura.

Daga bangaren Barcelona kuwa tun bayan data siyar da Neymar yakoma PSG masana suke ganin kamar abubuwa zasu cakude mata, wasu ma suna ganin kamar kungiyar bazata iya buga wani abin azo agani ba a kungiyar.

Hakan yasa itama kungiyar saboda tsoron haka ta bazama wajen neman dan wasan Liberpool, phillip Coutinho dan kasar brazil, wannan kokari nata kuwa bai samu nasara ba don sai da kungiyar takai tayin kudi har sau uku Liberpool din tana fatali da tayin inda kungiyar tace ita dan was anta bana siyarwa bane.

Amma a yan kwanakin nan anjiyo shugaban gudanarwae kungiyar ta Barcelona yana cewa Liberpool din ta bukaci kusan fam miliyan 178 akan dan wasan nata inda yace kungiyarsa bazata biya hakaba akan coutinho.

Shima kulob din A.Madrid yasamu kansa cikin wani hali bayan da har yanzu takunkumin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta samata na hanata siyan yan wasa har sai watan janairu duk da cewa kungiyar ta daukaka kara amma kotu tayi fatali da daukaka karar.

Hakan yasa har yanzu kungiyar bata kara karfin tawagar yan was anta ba, sai dai a ranar juma’ kungiyar ta cimma yarjejeniya da Chelsea wajen sake siyan tsohon dan was anta wato Diego Costa.

Gasar Laliga dai ankai wasanni biyar a halin yanzu kuma kungiypyi irinsu Real Soceidad, Sebilla da sauransu suma sun shirya don ganin sun buga abin ba’ayi tsammani ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Aguiro Zai Mutu Ya Na Cin Kwallo — Guardiola

Next Post

Sirrin Iyayen Giji… MATA SAI DA ADO

RelatedPosts

Diego Costa

Wace Kungiya Ce  Zata Dauki Diego Costa

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta...

Zaben Shugaban Barcelona

An Dage Babban Zaben Shugaban Barcelona

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bayar da...

ozil

Rikita-Rikitar Da Ta Baibaye Dangantakar Ozil Da Arsenal

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Kusan yanzu zamu iya cewa ta faru ta kare domin...

Next Post

Sirrin Iyayen Giji… MATA SAI DA ADO

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version