Nasir S Gwangwazo" />

Sheikh (Dr.) Yusuf Ali: Rayuwa Da Ayyukan Gina Al’umma (6)

Takardar da Dr. Bilkisu Yusuf Ali ta gabatar a taron kasa da kasa, don karawa juna ilimi a sashen koyar da harsunan Nijeriya da kimiyyar harshe na jami’ar jihar Kaduna ranar 2-4 ga Afrilu, 2016.

Cigaba daga makon jiya.

3.4.1.4 Zamantakewa

Zamantakewa ta iyali tana da mutukar muhimmanci a rayuwar dan’Adam ta yau da gobe, mafi kusanci a danganta ita ce ta auratayya kamar yadda Sheikh JDr. Yusuf Ali ya bayyana a wakarsa ta “Dangantakar da take cikin auratayya ta fi wacce take cikin haifayya”. Wannan waka gwanin mu ya yi amfani da wani salo da falsafa duk da kasancewarta waka,ce amma ya yi ta tamkar wasan kwaikwayo inda ya nuna an zo gunsa da fatawa kasancewar sa gwani kan soyayya inda yake cewa:
Watarana da daddare ne kwatsam a gidana,
Miji da mata sun ka zo su wajena,
Neman bayani kan irin zancena,
Don ko washe in sun wuce zaure na,
Shi sun ka lura na ke ta nanatawa .

Zan dau abin tamkar fa ni ka nufata,
In ka tuna j iya ma da ni ka kwatanta,
Ka ce kusanci na gurin matata,
Wane kusancina da ni da uwata,
Ka san kwa wannan dole kwai rikitawa

Da ka fadi haka sai na dinga riya wa,
Malam hala kwaya yake hadiyewa,
Ko ko ruwan kwalba yake korawa,
Don sanda zancen naka ke ta fitowa,
Ba na fahimtar kwai abin kamawa.

Na ce da shi daga yau ka bar haka wane,
Zato, ka tuba takarkarin zunubi ne,
Ballantana mai yin jawabin ni ne,
Duk karkaran nan an riga an gane,
In nai jawabi ba a kokwantawa.

Ta kara cewa dai da taushin murya,
Kayinta sunkuye don azabar kunya,
Kusantakar da take cikin auratayya,
Ta zarce wacce take cikin haifayya,
Mai hankali shi ne yake ganewa.

Dangantakar da ke cikin aurayya. 4-8 1973

Sheikh Dr. Yusuf Ali Mutum ne mai tsananin kishin harsehnsa da burin ya yi zarra a tsakanin harasa, inda yake cewa:
Roko nake harshe na Hausa ya je gaba,
Ya danne harshen duniya dannewa
Majalisa ta dinkin duniyar nan ta san das hi
Ya Rabbi amsa, Fatiha, Shafawa

Ta’aziyyar Garba ABCD.

3.4.1.5 Fadakarwa

Bahaushe mutum ne mai son taimakon dan’uwansa. Hanya ta nuna masa kauna shi ne ta taimakonsa musamman idan ya kasance gajiyayye. Don haka ya yi kira ga jama’a da nuiia musu muhimmancin taimakon juna a wakarsa me suna “taimakon gajiyayyu” Cikinta ya yi kira da nuna muhimmanci taimakon da wadanda za a taimakawa da ma inda za akai taimakon idan bukatar hakan ta so inda yake cewa: –
In kai niyyar bayar da kayan zakka,
Ga nakasassu ko abin sadakarka,
Hanya guda shida ga su nan a gabanka,
Gida, gun hira ko gun harkarka,
Gidan marayu ko gidan gajiyayyu

In me bara ya zo gunka ka sammar,
In akwai, in babu kadda ka korar,
Dadin bayani sai ka dubo surar,
Wadduha, wa ammassa’ila la tanhar,
Karfin batun Allah ya fi ya kayu

Abin al’ajab ka ga tasu dabi’ar,
In me bara ya yi sai kawai su hararar,
Sai bambami kenan kamar sa dokar,
Karshen abin har dai su zazzagar,
Su na fadin tafi can asara mayu.

Idan kana tsoran ka afka masifa,
Ko in kana matsa ne kana son kofa,
Ka juri yin sadaka ga kasassufa,
Ni Yusufu Ali ba sani zuzzurfa,
Ni nai kira ga taimakon gajiyayyu.

Taimakon gajiyayyu 20 – 24 (1980)

3.4.1.6 Madahu

Shehin yayi wakoki da yawa na yabon Annabi (S.A.W), Misali kadan daga cikinsu akwai.
Jama’a mui begen Mustapha,
Abin da haushi kwarai
Ka dauki yaro me dafa.
Baiwarka Daha nake jira
Ko za ta fado in cafa
Shi wanda ba shi da gaskiya
Ko da cikin ruwa yai zufa
A yaban Daha na Mariya
Ahalina bani rufa-rufa
Da kai na kan yi tawassali,
Da yin igasa Mustapha
Dan Bilki jikan Bilki baban
Bilki alkalin upper

3.4.1.7 Soyayya

Gwanina gwarzo ne a fagen soyyaya. Ya yi wakokin da dama kan soyayya wanda a yau in dai za a kawo misali na rubutattun wakokin soyayya na Hausa ba za taba tsallake shi ba. Wakoki ne da suka yi fice kuma ake alfahari da su duniyar adabi. Wakoki ne da suka sha warwara da kalalecewa a hannun dalibai da malamin nazari, an kawo ire-iren wadannan wakoki ga misali nan karara a littafi dausayin soyayya da littafm wakokin hikima. Shehin ya yi wakoki da daban – daban wadanda ke da jigon soyayya zalla misali;-
*Soyayar karya da ta gaskiya
*Allah da kansa ya kera ‘yar nan Dije
*Ina ma da a ce
*Lamarinki Dije yana da ban mamaki.
*So warware kudiri
*Mutuwa ce magani
*Dalilinki Nana na zam sarkin soyayya.
*Soyayyar karya da ta gaskiya da sauransu.

Misalin waka a jigon soyayya:
Ke Dije ga ni a durkushe,
Ina ta roko ko washe,
Har ga shi muryar ta dashe,
Makogwaro ya kekashe,
Ki taimaken ki yi jin kayi.

Idanuwa sun kakkafe,
Duk ba hawaye ya kafe,
Da a mike nake tafe,
A yanzu sai dai rarrafe,
Ki taimaken ki yi tausayi.

Jama’a gaba daya sun gujen,
In nai wajensu su bar wajen,
Dukansu sun ki su agajen,
In Dije ke ma kin gajen hakuri,
Da ni ya za na yi.

Don Allah Dije ki tausasa,
Wannan masifa ta isa,
Ga nesa ta zo kurkusa,
Saura kiris fa na karasa,
Ina zaton ba za na yi.

Wadansu na ta tafarfasa,
Don na ca ne so na kisa,
Fadi suke karya ta sa,
So bai hana wa ko ya sa,
Bare ya sa wani laulayi

A yanzu so dai na sani,
Cutarsa ba ta da magani,
Daci garas wane kuni,
Me yin sa ya fada bani,
Rayuwarsa ta yi karan-tsaye

“Soyayyar karya da ta gaskiya” 1-6

3.4.1.8 Tauhidi

Tauhidi shi ne kadaita Allah Sheikh Dr. Yusuf Ali ya yi wakoki ^arkashin wannan jigo misali.
Mu na gode Allah wanda ba shi da kishiya,
Ba shi uba Allahu ba shi mahaifiya.
Abinda ya sa kullum muke masa godiya
Domin ya nufemu da gane hanya ta gaskiya
Ga ma musuiunci ne tafarki na gaskiya
Ya ce wanda yai wani lahira za ya sha wuya
Cikin Ali-imrana aya ta sha takwas
Da aya tamanin da biyar ko da tambaya
Ga ma mu musulmi duk abuban da za mu yi
Mukan yi da hujja ne ta Allah cikakkiya
Abin da ya sa kullum muke kara karuwa
Wadansun mu na raguwa akan ba su gaskiya

3.5 Wa’azi
Yahaya (196:2004) ya bayyana ma’anar wa’azi ko wa’azu daga harshen Larabci, Hausa da larabci duk a wajansu kalma ce da ke nufin gargadi ko tsoratarwa.
A wancan lokacin ba wayewa kamar yanzu duk sanin ka duk lliminka. In j hdi:. Ba saninka aka yi ba wanda zai kira ka don wa’azi kuma shi ma a lokacin yana dar-dair yana. tsoron yin wa’azi cikin jama’a don haka bai fara wa’azi ba sai a 1972 albarkacjn j in muryarsa da aka yi a gidan radiyo na NBC wato radiyon Kano na yanzu. Yana gabatar da filin wakoki rubutattu ana kiran mawaka daban-daban suna karanta wakoki daga nan aka fara kiransu wuraren biki su karanta ko taro da sauransu.
Sheikh Dr. Yusuf Ali ya yi fice gaya wa wajen inganta rayuwar al’ummar da yake ciki ta hanyar kiransa ga addinin ubangiji. Shehin na kira ne ga kyawawan ayyuka da hani da mummunan halaye bilhasali ma kacokam lokacinsa in har aka dauke aikin gwamnati da ya yi ba shi da wani aiki fiye da wa’azi. Sheikh Dr. Yusuf Ali ya fara wa’azi ne- sakamakon jin muyarsa da ake yi a radiyo. Babba burin Sheikh Dr. Yusuf Ali tun a shekarar 1974 inda ya ambaci burin nasa shi ne wa’azi 1974 inda yake cewa:
Kamar yadda kowa akwai abin, da yake nufi,
Da zai dingayi matukar zamansa na duniya
Fa nima hakan nan akwai abifi da nake nufi
Nufi na taimakon musuiunci duk wuya
Kira ga musulmi da koyar da shi kwarai
Na ga duk a filin duniya sun fi moriya
Zan taimakawa musulunci akoina
Ta hannu ta alkalami ta zuci gaba daya
Zan taimakaw a musuiunci ako washe
Da rana da daddare gun tsaye ko ko kwanciya
Haka ne sana ’ata ba za ko tacanza ba,
Fa ko za a danne ni a yanka ya tunkiya
Haka ne dabi ’ata ba za ta canza ba fa,
Ko za a ce na bari a mai she ni miloniya
Kiran nan ga addini da shi na dogara
Duk rayuwata shi na dauke shi kariya

A wajejen 1980 aka fito da tsarin zuwa makaratar gaba da firamare don yi wa dalibai wa’azi saboda Bahaushe yace “ido wa ka raina” don haka ake kawo musu bakon ido don yi musu wa’azi.
A irin wannan wa’azi akan tattauna akan maudu’ai mabambarita misalan irin wadannan makarantu akwai makarantar kimiya ta Dawakin Kudu da makaranta mata ta shekara da WTC Kano wanda su kusan duk sati sai anyi wannan lacca din, don a WTC Kano har kirkirar wakokin yabon Annabi (SAW) suke dinga yi tare da yin gasa wanda duk a karkashi kulawarsa ne. Wanda wannan wakokin sun yi tashe kwarai a tsakanin 1987 – 1990 har maza su ma suke dauka suka kai ga kafa kungiyar Usshaku.
Akwai makarantar ‘yan mata WATC G/Dutse da Kura da Kabo da S.A.S da ABU Zaria da BUK da makaranatar ‘yan maCa ta Sumaila wannan lacca ta makaranatu duk sati ne.
A bangaren taruka kuwa na mauludi inda ake gayyatar Shehin don gabatar da Lacca nan ma ya ba da gudummawa kwarai da gaske don a watan muludin kadai shehin yana samin ‘ gayyata sama da 20,000.
Kafin watan azumi da kwana uku Shehin kan fara yin tafsir za a yi kwana Ashirin da Takwas cif ana gabatar da shi. Tafsirin Sheikh Dr. Yusuf Ali abin sha’awa ne kwarai don ba tafsir ne da za a ja a fassara kadai ba cikin gaggawa a biye a duk watan azumi, a’a Tafsir din ana bin sa cikin sannu da yi masa dalla-dalla duk fa’idar da take cikin ayoyin ko surar sai an bayyana tare da fadin bara da addu’o’i. Al’umma sun shaidi gwanin namu kan bayyana ilimi.

Exit mobile version