Nasir S Gwangwazo" />

Shekara Daya Da Kafa Ma’aikata: Shin Sadiya Farouk Ta Nuna Jinkai?

Jinkai

Bayan da al’amuran tsaro su ka kacame a Tarayyar Nijeriya, har ya jefa al’ummomin da lamarin ya fi shafa cikin halin kunci, fatara da talauci, musamman a yankin Arewa sakamakon hare-haren Boko Haram, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yawancin yankin, sai Gwamnatin Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta ga dacewar kafa ma’aikata sukutum, don nuna jinkai da tausayawa ga ainihin wadanda lamarin ya shafa.

A Agusta na 2020 a ka kaddamar da ma’aikatar, inda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadin ministocin da Shugaba Buhari ya aike ma ta, sai shugaban ya ga dacewar nada, Hon. Sadiya Umar Farouk a matsayin ministar ma’aikatar.

Kai tsaye za a iya cewa, nadin nata ya na nuna lallai shugaban ya aminta da ita kuma ya yi amanna da cewa, a lokacin da ta ke shugabantar hukuma makamanciyar wannan ma’aikatar ta yi namijin kokari kenan, don haka ya ga dacewar mika ma ta wannan jan aiki, wanda ya hada da nuna kyautayi ga duk wani dan Nijeriya da ya tsinci kansa a cikin yanayi maras dadi a gida da wajen kasar.

Kowa ya san yadda ’yan gudun hijira su ka fantsama ko’ina sakamakon yake-yake da tashin hankali da su ka tsinci kansu a garuruwansu. Don haka Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira, Hukumar Bada Agajin Gaggawa, Hukumar Hana Safarar Mutane, Hukumar Kula da Yankin Arewa maso Gabas, Hukumar Bada Tallafin Al’umma da Ofishin Mataimaki Kan Muradun Karni duka su na karkashin kulawar Ma’aikatar Jinkan.

Tamkar Gwamnatin Nijeriya ta san za a rina, watanni kadan da kafa wannan ma’aikata, katsam sai annobar cutar Korona ta barke a duniya bakidaya, inda ba ta bar Nijeriya a baya ba. Nan da nan al’amura su ka sauya, a ka rufe kasuwanci da sana’o’i da sunan dokar kulle, inda a ka tialsta wa kowa zaman dirshan a gida, illa kalilan daga wasu ma’aikatan tilas.

Hakan na nuni da cewa, aikin ma’aikatar Minista Sadiya karu, kuma lallai zai zama mai jan hankalin al’umma, domin ma’aikatar a ka dora wa alhakin samar da yanayin saukaka wa mutane halin da su ka tsinci kansu ta fuskar samar da tallafi ga masu sana’o’i.

Babban abin dubawa a tsawon shekara guda din nan shi ne, shin wannan minista ta yi aikin da a ka dora ma ta na jinkai ko kuwa?

Bayanan da wannan jarida ta samu ya nuna cewa, a karkashin shirin N-Power kadai matasa 500,000 ne su ka amfana, inda a ka tabbatar da cewa, tuni guda 109,823 daga cikinsu su ka samu nasarar kafa sana’o’in da su ka dore a cikin al’ummarsu. Za a iya cewa, wannan gagarumar nasara ce, idan a ka yi la’akari da matsalar A yanzu ma’aikatar ta Sadiya Farouk ta na daukar sababbin masu N-Power a jiko na gaba.

Wani abu da ya fi daukar hankali cikin irin tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa a karkashin wannan ma’aikatar a lokacin kullen annobar Korona shi ne, ciyar da dalibai da ke zaune a gidajensu. Mutane da dama na ganin cewa, tamkar karya kawai a ke shirgawa, don a handame kudin al’umma har a ke dora wa ministar laifi da zarge-zarge.

Sai dai kuma daga dukkan alamu mutane ba su fahimci yadda tsarin ya ke ba, musamman da su ka ji cewa, an ware makudan kudi, don ciyar da dalibai daga gida. Binciken da mu ka yi ya nuna cewa, an ware Naira 70 ga kowane yaro a ranakun karatunsu, don tabbatar da cewa, su na cigaba da cin abinci mai gina jiki, kamar yadda su ke yi tun kafin a fara dokar zaman gida, inda kowane yaro zai lashe Naira 4,200 kacal a wata.

To, sai dai kuma ba ma’aikar Sadiya ke da alhakin bin yaran ta na ba su abincin da kanta ba. Jihohi a ka damka wa wannan alhakin, domin su ne su ka fi kusa da su kuma makarantun masu ne. Don haka sun fi Gwamnatin Tarayya sanin inda su ke. Abin nufi a nan shi ne, duk jihar da a ka ga ba a bai wa yara abincin a gidajensu, to alhakin ya na wuyan gwamnatocin jihohin ne, domi ita ma’aikar Sadiya ta na ware kudinsu ne ta mika mu su tare da sanya mu su ka’idoji bisa amana.

Babban abin sha’awa shi ne, duk da cewa, an dora wa jihohi alhakin raba kayan abinci da ma wasu tallafin ga mabukata, amma ministar ta ziyarci akalla jihohi bakwai da kanta, don ziyarar gani-da-ido duk kuwa da bala’in annobar Korona da a ke fama da ita, inda ta ziyarci jihohin Imo, Ibonyi, Delta, Borno, Legas, Katsina da Kano, sannan kuma ta je Zamfara, amma a ka zargi gwamnan jihar da cewa, ya nemi yi ma ta kafar ungulu; lamarin da ya sanya matar ta nuna halin girma ta fice daga jihar, don gudun barkewar rikici.

A wata tattaunawa da a ka yi da Sadiya Farouk cikin makon nan a gidan talabijin na kasa, NTA, ta ce, “tsarin yadda Tarayyar Nijeriya ya ke ya sanya a kan samu kalubale wajen aiwatar da wasu ayyukan, saboda matakan gwamnatoci da a ke da su na Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi. A na samun kalubale kan wa ya fi dacewa ka damka wa amana irin wannan? A wane lokaci? A yaya za ka iya tabbatar da cewa wadanda su ka cancanta ne su ka amfana?”

Wannan furucin ’yar manuniya ce da ke nuna cewa, Allah ne kadai ya san irin kalubalen da wannan baiwar Allah ta fuskanta a aikin rabon tallafin nan da a ke yi na Korona. Watakila watarana za a ji, idan ta yi tsami.

Duk a cikin shekara guda din nan, sabuwar ma’aikatar ta kaddamar da wani shiri na inganta matsakaita da kananan sana’o’i mai taken GEEP, inda a ke tallafa wa ’yan Nijeriya akalla miliyan 37 ta hannun wakilai 4,325 da a ka tura jihohi 36 da Abuja. Yawancinsu sun amfana da rance maras ruwa na Naira 10,000 zuwa Naira 30,000. Babban abin sha’awa shi ne, kashi 54.3 mata ne, inda kashi 53 kuma matasa ne masu shekaru 18 zuwa 35. An raba sama da Naira biliyan 36.3 a wannan shirin.

Tunda dai ba yakin neman zabe mu ke yi wa Minista Sadiya ba, za mu iya tsayawa a nan da cewa, akalla jinkan ayyukanta sun bayyana; abinda ya yi saura shi ne, wadanda a ka damka wa wannan gingimemiyar amana a matakan jihohi, su yi abinda yakamata, kamar yadda ministar ta yi, don amfanin talakan Nijeriya.

Exit mobile version