Yayin da yake taya murnar cika shekaru 70 da fara gabatar da wani shahararren shirin rediyo na yara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga kwararru a fannin al’adun yara da su kara kaimi wajen renon matasa masu kwarewa domin ci gaba da bin tafarkin gurguzu.
Xi, ya yi wannan kiran ne a cikin wata wasikar taya murna da ya aika wa shirin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) mai suna “Xiaolaba”, ko “Little Trumpet” a yau Jumma’a. Ya yaba da jajircewar shirin a tsawon shekaru 70 wajen “bayar da labarai masu dadi ga yara,” wanda ya zama abokin rakiya ga matasa masu sauraro yayin da suke kara girma.
Wanda aka fara gabatar da shi a ranar 4 ga watan Satumbar shekara ta 1956, Xiaolaba shi ne shirin rediyo na farko a Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin wanda aka kebe musamman domin yaran da ba su kai shekarun shiga makaranta ba.
Tuni dai shirin ya gawurta ya zama babban shirin da ake watsawa a rediyo, da talabijin, da shafukan sada zumunta da shirye-shiryen yada labarai na cikin makarantu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














