ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
APC

Sakamakon korafe-korafe kan yadda aka tsara tawagar yakin neman zaben jam’iyyar APC na zaben 2027, na iya haifar da tashin hankali a fadar shugaban kasa, wanda ya tilasta yi garanbawul a tawagar.

Daga arewacin kasar, wata kungiyar matasa da ke goyon bayan sake zaben Shugaban kasa, Bola Tinubu, ta yi barazanar janyewa daga ayyukan goyon bayan Tinubu idan har ba a cire tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ba daga tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Haka Zalika, tsohon mai magana da yawun yankin kudu maso gabas na tawagar yakin neman zaben Shugaban kasa Tinubu da Shettima, Denge Onoh, ya soki sabon tawagar yakin neman zaben mai mambobi 223 da aka fitar don zaben 2027, yana gargadin cewa yadda aka tsara shi na iya rage damar Tinubu na sake samun cin zabe.

ADVERTISEMENT

Sai dai kungiyoyin hararen hula da lauyoyi da ‘yan adawa sun yi watsi da sanarwar da daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdul’Aziz Yari, inda ya ce jam’iyyar mulki za ta ci gaba da mulki har bayan shekara 2031, sun ce ikon siyasa na hannun masu zabe ne ba na kowace jam’iyya ba.

A lokacin watsi da rahotanni marasa kyau game da jerin tawagar yakin neman zabe, fadar shugaban kasa ta ce tsarin yana nan amma za a yi wasu gyare-gyare.

LABARAI MASU NASABA

 2027: Ƙaruwar Ta’addancin Siyasa Na Haifar Da Fargabar Yaƙin Neman Zaɓe A Jihohi

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

Kungiyar matasa da ke goyon bayan tazarcen Tinubu a 2027, a cikin korafita wanda aka aika wa shugaban jam’iyyar APC, ta ce kungiyar ta kasance mai jajircewa kan sake zaben Tinubu amma ba za ta iya ci gaba da fadakar da jama’a a karkashin tsarin da ake da shi ba.

Shugaban kungiyar, Sani Zangina, ya ce abin da kungiyar ke korafi kai shi ne, nada Sheriff a matsayin mai shirya yakin neman zabe na yankin arewa maso gaba na tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na APC na 2027.

Zangina ya ce, “Goyon bayanmu ga shugaba ba zai gushe ba, amma ba za mu iya ci gaba da bayar da goyon baya na son rai a karkashin tsarin da ke sanya Sheriff a gaba a yakin neman zaben a arewa maso gabas ba.”

A cewar kungiyar, rawar da Sheriff ke takawa a yakin neman zaben shugaban kasa na iya shafar APC da kuma kwarin gwiwar masu goyon bayan Tinubu wajen sake zabarsa.

Shi ma a cikin wata sanarwa, Onoh ya zargi cewa manyan masu ruwa da tsaki na APC da mabiya na asali daga kudu maso gabas an tauye su sosai a sabon tsarin tawagar yakin neman zabe.

Ya ce jerin tawagar yakin neman zaben akwai kabilanci da son zuciya, yana gargadin cewa wannan iya raunana goyon bayan shugaban kasa kafin zaben 2027.

Kwamitin yakin neman zabe, wanda aka sanar a karshen mako, Tinubu a matsayin shugaba, yayin da mataimakin shugaba kasa, Kashim Shettima, a matsayin mataimaki da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, a matsayin mataimakan shugaban.

APC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
     2027: Ƙaruwar Ta’addancin Siyasa Na Haifar Da Fargabar Yaƙin Neman Zaɓe A Jihohi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

MASU ALAKA

Yarjejeniyar Zaman Lafiya
Manyan Labarai

 2027: Ƙaruwar Ta’addancin Siyasa Na Haifar Da Fargabar Yaƙin Neman Zaɓe A Jihohi

October 4, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Tambarin Dimokuradiyya

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Next Post
Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye

Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.