Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Shugaban INEC Ya Yi Kira Ga Majalisar Tarayya Kan Kwaskwarimar Dokar Zabe

by Muhammad
January 11, 2021
in RIGAR 'YANCI
4 min read
INEC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Nasir S. Gwangwazo,

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga ‘yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la’akari da jam’iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Zabe garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zabe a kasar nan.

samndaads

Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin kaddamar da kwamitin hadin gwiwar kwararru na yi wa Dokar Zabe kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma’a.

Kwamitin Hadin Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Zabe da Al’amuran Zabe ne ya shirya taron tare da tallafin Cibiyar Tsare-tsare da Aikin Doka, wato Policy and Legal Adbocacy Centre (PLAC) da kuma Ofishin Harkokin Kasar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, wato UK Foreign and Commonwealth Debelopment Office (FCDO).

Yakubu ya ce garambawul din ya zo a kan kari, kuma abu mafi muhimmanci shi ne lallai a tabbatar da cewa gyare-gyaren sun yi tasiri, kuma an yi su ba tare da kallon kowace jam’iyya ba, sannan a cire duk wata rarrabuwar kai, kuma a kammala su akalla daga yanzu zuwa watanni hudu na farko na shekarar 2021.

Idan an tuna, tun a cikin 2020 ne shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi alkawarin cewa Majalisar Tarayya za ta bada hadin kai wajen zartar da gyaran Dokar Zabe ya zuwa karshen watanni hudu na farko na shekarar 2021.

Shugaban na INEC ya yi na’am da sabon yunkurin da kuma sadaukarwar da shugabannin Majalisar Tarayya su ka nuna wajen yi wa tsarin dokokin gudanar da zabe kwaskwarima.

Yakubu ya ce sabon hobbasan da majalisar ke yi ya zo a kan kari kuma tilas ne a ci gaba da shi tare da aiwatar da shi a cikin tunanin waiwaye da kuma hanzari.

Ya ce lallai ne a tabbatar da yunkurin ya tafi bisa hanyar kammaluwar sa, hanzari, saka hannu da tunanin dabaru.

Yakubu ya ce hukumar ta sadaukar da kai sosai ga tabbatuwar aikin garambawul din kuma za ta ci gaba da bada shawarwari da za su taimaka wajen ingantuwar harkokin zabe a kasar nan.

Ya kara da cewa gyara tsarin dokokin zabe ba wai zai haifar da sauyi farat daya wajen aikin gudanar da aikin zabe ba.

Wani memba a kwamitin kwararrun, Malam Sadik Mu’azu, ya yi nuni da cewa daya daga cikin alfanun yi wa Dokar Zabe gyaran fuska shi ne zai tattaro dukkan gyare-gyaren a cikin kundi guda daya.

Mu’azu ya ce babban burin garambawul din shi ne domin a tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa sun kula da hakkin maza da mata tare da kawar da duk wani nau’i na bambanci daga cikin jam’iyyun siyasa.

Ya ce, “Dokar ta bukaci dukkan jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa shugabanni mata su ne mata ba maza ba kuma dukkan shugabannin matasa za su kasance ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 45 daga ranar da aka yi zabubbukan wadannan mukaman.

“Kuma dokar ta na so a kara yawan kudin da ‘yan takarar zama Shugaban Kasa ko Gwamna ko Sanata ko dan Majalisar Tarayya za su iya kashewa a kamfen.

Ya ce: “An kara kudin da dan takarar Shugaban Kasa zai iya kashewa daga naira biliyan daya zuwa naira biliyan 5, sannan an kara na dan takarar gwamna daga naira miliyan 200 zuwa naira biliyan 1, sai kuma aka kara na dan takarar Sanata zuwa miliyan 100, na dan Majalisar Wakilai kuma zuwa miliyan 70.”

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Hukumar Zabe a Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce idan an zartar da dokar kuma aka amince da ita, to za ta taimaka gaya wajen sauya fasalin siyasar kasar nan.

Ya ce: “Ba shakka, yi wa Dokar Zabe garambawul zai yi tasiri mai kyau matuka a kan hanyoyin gudanar da zabe wadanda sun sha gamuwa da kalubale a baya tare da tada muhawarori wadanda su ka yi barazana ga bukatar yin zabe cikin ‘yanci, adalci da inganci.”

Ya ce an kaddamar da Kwamitin Kwararru din ne domin a cimma iyakance lokacin da za a amince da dokar ya zuwa karshen kwatar farko ta shekarar 2021.

Shi kuwa Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, alkawari ya yi na yin aiki tare da kwamitin kwararrun domin tabbatar da ba a samu cikas ba wajen samun amincewar shugaban kasa ga dokar.

Malami, wanda mai taimaka wa shugaban kasa ta musamman kan gyaran fuskar harkokin shari’a da hulda da kasar waje, Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu ta wakilta, ya ce, “Zan ci gaba da aiki kafada da kafada da Majalisar Tarayya don tabbatar da a karshe kwaskwarimar ta samu amincewa kamar yadda aka tsara.

“Na tuna da cewa ba a dade da gama zabubbukan 2015 ba, Shugaban Kasa ya amince da kaddamar da kwamitocin gyaran fuskar tsarin mulki da dokokin zabe a cikin 2016, kuma mu na ta aiki tare da Majalisar Tarayya kuma mun fito da dokoki hudu wadanda Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta yarda da su kuma ta aika da su zuwa Majalisar Dokoki.”

Shi ma a jawabin sa, Babban Daraktan PLAC, Mista Clement Nwankwo, ya bayyana jin dadi kan ganin za a zartar da dokar a cikin kankanen lokaci.

Ya ce, “Sakamakon ganin yadda aka kasa a yunkurin baya na rattaba hannu kan Dokar Zaben a cikin 2018, a bayyane ya ke cewar wannan sadaukarwar ta samu amincewar kowa da kowa daga kowane bangare, wanda hakan ya nuna kenan yanzu mun samu sabuwar Dokar Zabe.

“Tare da goyon bayan Ofishin Harkokin Kasar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, mun samu nasarar yin hadin gwiwa da Majalisar Tarayya don ganin an cimma burin da majalisar ta ke so a cimmawa.”

SendShareTweetShare
Previous Post

Allah Ya Toni Asirin Duk Mai Hannu A Ta’addancin Katsina – Addu’ar Sakataren Gwamnatin Jihar

Next Post

’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Satar Yara Bakwai A Zamfara

RelatedPosts

’Yan Sandan Italiya

’Yan Sandan Italiya Sun Kama ’Yan Nijeriya 16 Masu Sana’ar Miyagun Kwayoyi

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Rahotanni daga Kasar Italiya sun zo da ingacin cewa a...

miyagun kwayoyi

NDLEA Sun Cafke Mutum Uku Da Hodar Iblis A Legas

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA),...

’Yan Fashi

’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan Dan Uwan Akanta Janar Na ​​Imo

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

’Yan sanda sun tabbatar da kisan dan uwan ​Akanta Janar...

Next Post
Yara Bakwai

’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Satar Yara Bakwai A Zamfara

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version