Shugaban Jami’ar Dutsinma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Bichi, ya zargi wasu ma’aikatan jami’ar da taimakawa ƴan bindiga da bayanai. Yankin na fama da hare-haren ƴan bindiga inda ake garkuwa da ɗalibai, da ma’aikata, da kuma iyalansu.
A wani hari na baya-bayan nan, an kashe Dr. Tiri Gyan David, shugaban sashen Tattalin Arzikin Noma, Yada Albarkatun Ƙasa, da Raya Karkara, sannan kuma an yi garkuwa da ƴaƴansa.
Farfesa Bichi ya bayyana cewa shugabancin jami’ar ya gano ma’aikatan da ake zargi da taimakawa ƴan bindiga da bayanai kuma sun miƙa lambar wayarsu ga hukumar tsaro domin bincike. Duk da haka, Farfesan ya nuna damuwarsa kan rashin bayyana cikkaken rahoto daga hukumar tsaro. Ya jaddada cewa jami’ar na ƙoƙarin hana sake faruwar irin wannan al’amari, amma lamarin na ƙara ta’azzara.
- Jami’ar ‘Yar’aduwa Ta Katsina Ta Kama Hanyar Rugujewa – ASUU
- Shekara Ɗaya A Ofis: An Buɗe Gasar Cin Kofin Babban Hafsan Sojojin Nijeriya A Katsina
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana cewa ba su da masaniya kan waɗannan zarge-zarge amma sun yi alkawarin gudanar da bincike. Ya buƙaci jama’a da su ba da bayanan da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin.