Rabiu Ali Indabawa" />

Shugaban Uganda Ya Haramta Sanya Riga Dake Hade Da Hula

A can kasar Uganda kuma, jiya Litinin shugaban kasar Yoweri Musebeni ya bukaci a haramta amfani da rigunan nan da ke hade da hula da ake cewa hoodie da turanci kuma ya bukaci a Makala na’urorin bincike a kan dukkan abubuwan hawa. Ya dauki wannan matakin ne biyo bayan kashe wani dan majalisar a ranar Juma’a.

Kafofin yada labaru a yankin sun bada labarin cewa, a ranar Juma’a da maraice aka harbe Ibrahim Abariga wani dan majalisa, a lokacin da aka yi zargin cewa wasu mahara sun yi wa motar sa kaca kaca da harsashe a lokacin da ya doshi gidansa dake kimamin kilomita goma daga baban birnin kasar. Haka shi ma mai tsaron lafiyar sa mai suna Sa’id Kongo Buga shi ma an kashe shi.

Shedun gani da ido sunce mahara biyu a kan babur sanye da rigunan dake hade da hula suka tare motar dan majalisar Abariga.

A wajen jana’izar Abariga jiya Litinin, shugaba Musebeni cikin fushi ya yi alkawarin cewa za a gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin. Shugaban ya yi kukar cewairin rigunan dake hade da hula na boye fuskokun mahara, al’amarin dake dagula gano, bata garin a saboda haka an haramta amfani da irin wadannan riguna a kasar.

Exit mobile version