Abiola Issah ita ce matukiyar jirgin kasa ta farko a kasar Nijeriya. A shekarar 2013, ta shiga shirin bayar da horo da kamfanin CCECC na kasar Sin ya shirya game da guraben aikin yi da za a samar ga al’ummar Nijeriya wajen gudanar da layin dogo na birnin Abuja, wanda kamfanin ya dauki nauyin ginawa. Bayan tsawon shekaru biyar, Abiola ta zama matukiyar jirgin kasa ta farko a kasar Nijeriya, har ma tsohon shugaban kasar marigayi Muhammadu Buhari ya gana da ita. Abiola ta ce, kamar sauran mutane irinta da dama, wannan layin dogo ya canja rayuwarta, ta ce, “sufuri ya zama tushen ci gaban kasa. Hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin a fannin sufuri, ba kawai ya inganta ababen more rayuwar kasashen ba, ya kuma farfado da tattalin arzikinsu da kuma samar da guraben ayyuka ga al’ummarsu. Matasa irina mun koyi fasahohi har ma mun samu ayyukan yi.”
Abin da ya faru ga malama Abiola kyakkyawan misali ne da ya shaida yadda ci gaban kasa ya taimaka ga inganta hakkin dan Adam, wato manyan ababen more rayuwa sun sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin kasa, tare da samar da guraben ayyukan yi ga al’ummarta, kuma ta hakan an kyautata rayuwar al’umma, baya ga karewa da inganta hakkin dan Adam.
Ke nan hakkin rayuwa da kuma hakkin ci gaba sun kasance na farko daga cikin hakkokin dan Adam. Idan babu ci gaban kasa, babu tushen sauran hakkokin dan Adam ke nan. A don haka ne, a gun taron kara wa juna sani tsakanin Sin da kasashen Afirka kan hakkin dan Adam karo na farko da aka gudanar kwanan baya a birnin Addis Ababa, mahalarta taron sama da 200 da suka zo daga kasashen Sin da Afirka kimanin 44, suka yi musayar ra’ayoyi game da batun “hakkin samun ci gaba”. Matsayar da aka cimma a wajen taron ta kuma yi nuni da cewa, ci gaban kasa tushe ne na warware dukkanin matsalolin hakkin dan Adam.
A hakika, kwarewar kasar Sin a fannin inganta hakkin dan Adam ta hanyar raya ci gaban kasa, tana da muhimmiyar ma’ana ga kasashen Afirka wajen fid da kansu daga kangin talauci da kuma tabbatar da hakkin dan Adam. A game da hakan, Prof. Melha Rout Biel, shehun malami a cibiyar nazarin tsare-tsare da manufofi ta kasar Sudan ta Kudu ya yi nuni da cewa, “Kasashen Afirka da Sin dukkansu sun taba fuskantar koma baya sakamakon katsalandan da wasu kasashen suka yi musu. Batun hakkin ci gaba da kasar Sin ke magana a kai, abu ne da ya faru gare mu, don haka, muke goyon bayan kasar Sin wajen kokarin tabbatar da hakkinmu na ci gaba.”
Har kullum, kasar Sin na dukufa a kan “inganta hakkin dan Adam ta hanyar raya ci gaban kasa”, ta kuma gabatar da shawarar raya kasashen duniya, don “kar a bar wata kasa a baya”, kuma ta hanyar inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka a wannan fannin tare da cimma kyawawan nasarori. Misali kasar Sin ta taimaka wajen horar da dimbin kwararru na kasashen Afirka, don inganta kwarewar kasashen wajen tabbatar da ci gabansu. A kwanan nan, layin dogon Mombasa zuwa Nairobi da kamfanin kasar Sin ya gina ya cika kwanaki 3000 da fara aiki, wanda ya rage kudaden jigilar kayayyaki kimanin kaso 40% ga al’ummar wurin, tare da samar musu guraben aikin yi dubu 74, kuma hakan ya tabbatar da hakkin ci gaban al’ummar kasar. Har wa yau, Kasar Sin ta kuma yi gine-ginen ababen samar da makamashi mai tsabta sama da 100 a Afirka, ciki har da tashar samar da lantarki daga karfin ruwa ta Zungeru, wadanda suka samar da karfi ga kasashen Afirka wajen tabbatar da dauwamammen ci gabansu.
Duk da haka, kasashen yamma sun sha yin amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin makami wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe masu tasowa. A Afirka, kasashen yamma su kan bayar da gudummawar tattalin arziki bisa gindaya sharuda kan batutuwan hakkin dan Adam, sai dai irin katsalandan da suke yi ta fakewa da batun hakkin dan Adam kan haifar da munanan illoli ga kare hakkin dan Adam a kasashen Afirka. Don haka, a matsayar da aka cimma a gun taron, Sin da kasashen Afirka sun jaddada cewa, suna goyon bayan kasa da kasa su zabi hanyar da ta dace da yanayin da suke ciki, kuma suna masu adawa da siyasantar da batun hakkin dan Adam ko kuma mai da shi tamkar makami.
A yayin da malama Abiola Issah ke samun horo a kasar Sin, ta taba shiga jirgin kasa mai saurin tafiya na kasar. Ta ce ba ta taba ganin jirgi mai sauri haka ba, kuma fatan ta shi ne, wata rana Nijeriya ma ta samu irin jirgin, kuma ta zama matukiya ta farko ta irin wannan jirgin kasa a gida Nijeriya. A ganina, yayin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, tare da tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, burinta zai cika nan bada jimawa ba, kuma Sin da kasashen Afirka za su tabbatar da ci gabansu na bai daya bisa hadin gwiwarsu, a yayin da za su dada kyautata rayuwar al’ummunsu da kuma kara inganta hakkin dan Adam bisa ci gaban kasashensu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp