Manhajar “TIKTOK” da ta yi matukar samun karbuwa tsakanin masu amfani da yanar gizo a Amurka, na fuskantar barazanar daga gwamnatin kasar, inda gwamnatin ke ce idan ba a sayar da ita ga bangaren Amurka ba, za ta haramta amfani da ita baki daya, bisa dalilin tsaron kasar Amurka. Saboda haka, masu amfani da wannan manhaja sun yiwa kansu lakabi da “’Yan gudun hijirar TIKTOK”, inda suke rungumar wata manhajar sada zumunta ta daban ta kasar Sin, wadda ake kira da “Red Note”, matakin da ya sa masu amfani da yanar gizo na Sin da Amurka, suke yin mu’ammala mai zurfi a wannan danali.
Mu’ammala mai zurfi da ake yi sakamakon yawan shigar masu amfani da yanar gizo daga Amurka cikin manhajar “Red Note”, da kuma kwararar dimbin ‘yan yawon bude ido na kasashen waje cikin kasar Sin bisa manufar shiga kasar ba tare da bukatar visa ba, da gwamnatin Sin ke aiwatarwa, sun bayyana cewa, burin kara mu’ammala tsakanin jama’a zai cika, duk da manufar matsin lamba da ita Amurka ke dauka. A bangare na daban kuma, Sin mai bude kofarta ga ketare, na samar da wani dandali mai kyau na inganta mu’ammalar jama’ar duniya.
Sin na maraba da jama’ar duniya, don su fahimci ainihin yanayin da kasar ke ciki a dukkan fannoni. (Mai zane da rubutu: MINA)