A karkashin shawarar inganta ci gaban duniya ko GDI da kasar Sin ta gabatar, gwamnatin Sin ta gudanar da muhimman ayyukan hadin gwiwa sama da 2,000 tare da sassa daban daban, ayyukan da kai tsaye suka amfanar da al’ummu a sama da kasashe da yankunan duniya 120. Wadannan ayyuka sun samar da wani ginshiki na kaiwa ga cimma manufofin dake kunshe cikin ajadar MDD ta wanzar da ci gaba nan zuwa shekarar 2030.
Cikin wadannan shirye-shirye, a kusa da gida kasar Sin ta yi hadin gwiwa da asusun yara na majalisar dinkin duniya tare da larduna da dama na kasar Laos, wajen aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki ga yara kanana. Karkashin hakan, an tanadi hidimomin tantance lafiya, da na jinya mai inganci, da kandagarkin cututtuka, matakan da suka ceto rayukan yara masu fama da karancin koshin lafiya.
Idan muka leka kasar Habasha ta shiyyar kahon Afirka, za mu tarar da cibiyar horar da sana’o’i ta Luban, wadda kasar Sin ta kaddamar a shekarar 2021, cibiyar da tuni kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta jinjinawa, tare da bayyana ta a matsayin dandalin samar da kwarewa ga daukacin al’ummun Afirka. A cibiyar, ma’aikata da ake horar wa na samun dabaru da sanin makamar aiki, wadanda ke taimaka musu a fannin kara zamanantar da masana’antun kasashensu.
A yanzu haka, shawarar GDI, na kara samun karbuwa tsakanin sassan kasa da kasa. Inda tuni kasashe sama da 130, da hukumomin kasa da kasa suka bayyana amincewa da ita, tare da shiga hadin gwiwa da ita. A daya bangaren kuma, ta samu damar yin kawance da kusan abokan hulda 100, wadanda suka sanya hannu kan takardun yarjejeniyar hadin gwiwa na musamman na shiga ayyukan da kasar Sin ta tanada karkashin shawarar. Har ila yau, akwai wasu kasahe 88 da suka shiga rukunin kawance na shawarar ta GDI, yayin da tsarin aikin majalisar dinkin duniya mai nasaba da shawarar ya samu shigar hukumomin ingiza ci gaba guda 20.
Shawarar GDI ta dace da dadaddiyar manufar kasar Sin ta yin tafiya tare da dukkanin sassan duniya a fannin neman hanyoyin bunkasa ci gaba. Kuma mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin ci gaba da aiwatar da matakai daban daban na ingiza ci gaban duniya, da aiki tare da dukkanin sassa, wajen karfafa karsashi da hadin kai, da nufin dinke dukkanin bangarori, ta yadda za a kai ga cimma karin moriyar bai daya ga dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)














