Connect with us

RAHOTANNI

Sin Na Kokarin Kafa Kawancen Tattalin Arziki Na Arewa Maso Gabashin Asiya

Published

on

A ranar 12 ga wata aka bude cikakken taro karo na hudu na dandalin tattaunawar harkokin tattalin arziki na gabashin duniya, inda shugaban kasar Sin Di Jinping ya yi jawabi mai taken “more sabuwar damar bunkasuwa a yankin gabas mai nisa na Rasha, da samar da kyakkyawar makoma a arewa maso gabashin Asiya”. Jawabin da ya taimaka ga aikin kafa kawancen tattalin arziki na arewa maso gabashin Asiya, da inganta dauwamammen ci gaba a fannoni daban daban a yankin.

A cikin jawabinsa, shugaba Di Jinping ya gabatar da buri na neman kafa kawancen tattalin arziki na arewa maso gabashin Asiya. A hakika dai, aikin na da tushe mai inganci. Na farko, akwai dimbin albarkatun halittu a yankin arewa maso gabashin Asiya, inda har ma a kan kira yankin gabas mai nisa na Rasha da “wuri guda kacal a duniya mai kunshe da albarkatun da ba a binciko ba”. Na biyu, karfin nazarin kimiyya da fasaha na yankin arewa maso gabashin Asiya yana gaba a duniya, kasashen Sin da Rasha da Japan da Koriya ta Kudu sun fintinkau a wannan fannin. Na uku kuma, yankin na da cikakken jari, musamman jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje wanda ya kasance wani muhimmin ginshikin taimaka wa karuwar yawan jari da aka zuba a kasashen waje kai tsaye a duk duniya. Kamar yadda Shugaba Di Jinping ya fada, “yankin arewa maso gabashin Asiya mai jituwa, inda ake samun amincewar juna da hadin kai sosai da ma kwanciyar hankali ya dace da muradun kasa da kasa da ma fatan duniya” ,”Kasashen da ke yankin na da karfin raya fifikonsu wajen kyautata hadin kansu daga dukkan fannoni”.

Amma ta yaya bangarori daban daban za su zurfafa hadin gwiwarsu bisa sabon halin da ake ciki? Game da wannan, Shugaba Di Jinping ya gabatar da shawarwari na “hada shirye-shiryen neman ci gaba na kasa da kasa tare”, da “ba da muhimmanci kan raya muhimman ababen more rayuwa da ke shafar kasashen biyu”, da “samar da ‘yanci da saukaka harkokin cinikayya da zuba jari”, da ma “kara karfafa hadin gwiwa da wasu kasashe”. Ba shakka, wadannan shawarwari na da muhimmiyar ma’ana. Yanzu an riga an samu wasu tsare-tsaren hadin gwiwa a tsakanin bangarori biyu ko bangarori da dama a yankin arewa maso gabashin Asiya. An samu nasara wajen raya hanyar tattalin arziki a tsakanin Sin da Rasha da Mogoliya, kuma ana gaggauta yin shawarwari game da kafa yankin ciniki cikin ‘yanci a tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu. Duk wadannan sun taimaka ga samun bunkasuwa mai dorewa a yankin, da kuma samar da fasahohi ga zurfafa hadin gwiwarsu a yankin.

Abu mafi muhimmanci shi ne, shawarar “Ziri daya da hanya daya” ta samu karbuwa sosai a yankin arewa maso gabashin Asiya. Dukkan kasashen da ke yankin na nuna aniyar ta shifa cikin shawarar. Shugaba Di Jinping ya nuna cewa, Sin da Rasha sun himmatu wajen hada shawarar da kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya tare, wanda kuma ya riga ya samu wasu muhimman ci gaba. Sin na son hada shirinta da na ragowar kasashen duniya cikin shawarar. Ba shakka lamarin zai kara samar da dama ga aikin kafa kawancen tattalin arziki na yankin arewa maso gabashin Asiya.

Idan mu ka yi hangen nesa za mu ga cewa, kawancen tattalin arziki na arewa maso gabashin Asiya mai salon bude kofa zai kara kawo wa jama’ar yankin alheri, kana zai kasance wani muhimmin karfi wajen raya tsarin dokokin duniya mai adalci yadda ya kamata. (Kande, Zainab, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: