Ma’aikatar kula da muhallin halittu da muhalli, da kwamitin tsara manufofin raya kasa da aiwatar da sauye-sauye ta kasar Sin, sun fitar da tsarin hadin gwiwa na sanya ido don inganta muhalli da muhallin halittu, wanda za a aiwatar karkashin tsarin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, wato tsakanin shekarar 2026 zuwa 2030.
Tsarin zai mayar da hankali kan ingiza gina shirin zamani na sanya ido a fannin shirin cimma nasarorin zamani, na inganta muhalli da muhallin halittu nan zuwa shekara ta 2030, tare da gabatar da muhimman nauyaye-nauyaye guda biyar da ayyuka guda shida cikin wa’adin.
Karkashin shirin, Sin na da burin kammala hadadden tsarin sanya ido kan ci gaban yanayin muhalli da muhallin halittu, da karfafa matakan gargadi na gaggawa, da ikon sanya ido kan sabbin abubuwa masu gurbata muhalli, da sinadaran karafa masu hadari, da sauran abubuwa masu lalata muhallin halittu, da cimma manyan nasarori a muhimman fasahohin sanya ido. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)














