A yau Jumma’a, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da matakin sanya kamfanoni 14 na Tarayyar Turai (EU) cikin jerin wadanda aka hana fitar masu da kaya, domin kiyaye tsaron kasa da muradun kasar, tare da cika alkawuran kasa da kasa na hana yaduwar makamai.
An haramta wa masu gudanar da hada-hadar fitar da kayayyaki su fitar da kayan da ake iya amfani da su ta fuskoki biyu ga kamfanonin da suka hada da Lafert S.p.A., Garnet S.r.l., Sindlhauser Materials GmbH, Rheinmetall AG, Antraco Chemie-Handelsgesellschaft mbH, InPACT S.A. da kuma kamfanin III-V LAB, kamar yadda sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce an dauki matakan ne domin mayar da martani kan matakin da EU ta dauka na sanya kamfanoni 14 daga babban yankin Sin da kuma Hong Kong cikin sabon takunkumin da ta kakaba wa Rasha.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa, an dauki matakan ne bisa dokoki da ka’idojin da suka dace, ciki har da dokar hana fitar da kayayyaki daga kasar Sin da kuma ka’idar hana fitar da kayayyakin da ake iya amfani da su ta fuskoki biyu zuwa kasashen waje. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













