ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

by Shehu Yahaya
2 months ago
NDC

Yayin da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027 kara karatowa, jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NDC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kawo ziyarar aiki Jihar Kaduna inda ya gana da shugabanni da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NDC da kuma kungiyar Obidient

Wakilinmu SHEHU YAHAYA ya samu damar zantawar da Kwankwaso jim kadan bayan kammala ziyarar inda ya yi  bayani kan dalilin ziyararsa Kaduna, yanzu ta tabbata cewa jam’iyyar APC ba zata iya rike Nijeriya ba duba da yadda abubuwa suka tabarbare. Ga yadda hirar ta kasance:

Ka zo Jihar Kaduna Kuma ka gana da bangarori na jam’iyar NNPP, NDC da masu tafiyar OK na Peter Obi za mu so muji menene dalilin wannan hadduwa taku a Jihar Kaduna?

ADVERTISEMENT

Da farko ina godiya ga Allah kuma ina gode wa dukkanin jama’ar Kaduna musamman wannan sassa namu da muke aiki dasu na Kwankwasiya da ita jam’iyyar NDC wanda mun tattauna dasu kuma dama shi ne dalilin wannan zuwa domin mu gaisa .

Na dade kwarai da gaske rabon da na zo wannan jiha ta Kaduna. Yawanci, yanzu mun fi tafiya a jirgi sabanin da da yawa duk wanda zai tafi Kano ta kasa ake bi.

LABARAI MASU NASABA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

Alhamdulillah gashi mun biyo mun zo kuma mun ga masoya mun kuma tattauna da abokan tafiyarmu ta yadda za su yi dammara su fara aiki, su hada kan mutane a wannan jiha domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta NDC ta kaiga nasara

Kuma bayanan da na ji sun bani karfin gwiwa a kan wannan tafiya ta bangaran Kwankwasiya da obi-dient wannan abin sha’awa ne kuma muna kira  ga jama’a dasu tabbatar da cewa sun ba da goyan baya musamman a yanzu maganar rijistar  katin masu zabe.

Kuma nan da kwana tara ana tunanin za a gama, Don haka Ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna da magoya bayanmu dama wadanda suke ganin basa goyon bayanmu. Saboda yanzu muna da lokaci daga nan zuwa Janairu mutanen Nijeriya musamman jama’ar Jihar Kaduna za su gane cewa akwai bukatar canji kuma na alheri wanda za a dakile wannan matsalar rashin tsaron da muke fama dashi sa’annan muna taya jama’ar Birnin Gwari da sauran kananan hukumomi da suke ta fama da wannan matsala da kuma matasa, abin takaici ne da damuwa yadda al’amura suka lalace a Nijeriya ta kowane bangare musamman fannin tsaro da tattalin arziki, amma abin mamaki da damuwa sai ya zamana wadanda ke rike da madafun iko ko a jikinsu.

Babu wani abu na ci gaba guda daya da zaka iya kawo cewa gwamnatin APC ta samar a Nijeriya, a kullum tafiyar kura ake yi, an mayar da mutane bayi a kasar su ta haihuwa, kuma lokaci ya gama kurewa jam’iyyar APC ya tabbata ba za ta iya ba, saboda haka lokaci ya yi da talakawa za su yi ƙumumuwa domin kawar da ita.

Yanzu halin da ake ciki kowa yana ji ajika donn haka lokaci ne da dukkan wani talaka da duk wani mabukata za su hada kai a kawo canjin da ya kamata,

Jam’iyar NDC  tana fama da rikice-rikice na shugabanci, ‘yan takara da sauransu. Shin baka ganin hakan ba zai kawo muku cikas a tafiyar ku ?

Kasan ita jam’iya idan kaga ana rigima a cikinta  to an hadu ne yayin da  wasu jamiyya  suna can suna neman wanda za su tsayar a matsayin kansila amma babu, wasu jam’iyyun ma indan aka  fadi sunansu ba’a san suba saboda  yanzu muna da jam’iyyun siyasa kusan guda 20 amma idan ka kirga jam’iyyu biyar  ko bakwai daga su shike nan ragowar jama’a basu  san sauran ba.

Kaga jam’iyyar NDC ita ce ‘yar autansu wacce a watan Disambar bara aka yi mata ragista gashi yanzu muna watan Juli  kusan rabin shekara kenan amma gashi ta kewaye ko ina a Nijeriya saboda an yi sa’a mu daga bangaranmu mun shigo da Kwankwasiya cikinta. Kuma babu wata unguwa kowani gida a Arewacin Nijeriya da zaka je ka ji babu Kwankwasiya kuma a inda babu Kwankwasiya sai kaga akwai Obi-dient wannan hadaka da muka yi muna ganin Allah ya kawota ne domin ceto wannan kasa tamu . Don haka ina kira ga mutane kowa ya ba da gudunmawa kamar yadda muke wannan fafutuka da wannan gwagwarmayar domin tabbatar da talakan kasar nan musamman nan Arewa duk da gashi irin matsalolin da muke fama da su sunata shiga kudu amma dai inda ake fama da wahalar sosai shi ne Arewa.  Saboda haka muke Kira ga jama’a wadanda ba su yi rijista ba su yi. Kuma su hanzarta su yi rijista da jam’iyyar mu ta NDC da ake yi yanzu.

Ya tabbatar da jam’iyar mu itace tafi kowacce  jam’iyya samun daukaka da  karblbar mutane wannan abune na alkhairi Kuma muna godewa alummar kasar nan  akan wannan goyan bayar da suka bamu

Dan Arewa ya so jin ace Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai tsaya takarar Shugaban Kasa kawai  sai  aka ji Kwankwaso zai fito takarar mataimakin shugaban kasa. Kana ganin wannan zai sanya ku samu abin da kuke  bukata  a zaben 2027?

Kwarai kuwa za a samu, ai kasan shi  dan Adam kullum sai ka yi lissafi da nazari ka duba ya zaka bada gudummawa. Ni ba neman mukami ba ne a gaba na, babban abin da nake fata shi ne yadda za a samu sauyi a kawar da muguwar gwamnati, saboda haka matukar zan bayar da tawa gudummawa to ban damu da sai na samu mukami ba.

Lokacin da na kasa dukkanin ‘yan takarar neman shugabancin Nijeriya a faifai, sai na ga Peter Obi shi ne ya dace da irin tsarin da nake dashi na ci gaban kasa da inganta rayuwar jama’a, wannan ya sa na amince muka kulla kawance, domin kamar yadda kowa ya sani ne manufar tafiyar Kwankwasiyya shi ne mayar da wanda ba kowa ba ya zama kowa, shi ya sa a tsarinmu muka ba ‘yanyan talakawa dama, muka dauki nauyin karatun su a gida da waje wanda a yau an wayi gari sun zama wadanda al’umma suke alfahari da su, to idan har za mu iya yin haka a Kano me zai hana hakan ta faruwa a Nijeriya?

Mu tafiyar da muke ta akida ce ba tafiya muke ta kudi ba saboda inda tafiyar kudi muke mun san inda  kudadden suke, gasu nan a rantosu a sayar da Man fetur a karci kudi ayi abubuwa da su babu iyaka. Amma Idan ka zaga a zahiri ba zaka gani ba, toh, inda ace kudi muke nema da sai mubi Yarima asha kida. Ma’ana muma sai mubi wannan tsarin saboda  wannan ba itace a gaban mu ba, mu Allah ya rufa mana asiri kuma Allah ya ba mu dama damar da muke murna da ita.

Yadda muke ba da shugabanci ga mutanen da wadanda idan sun yi maganarma ba za a ji su ba ko ihu suka yi ba ji za a yi ba saboda haka muke godiya ga Allah da ya ba mu rai da lafiya kuma ya ba mu wannan tunani da muke wannan aiki da yake dadada mana rai duk da mun sani kowa ya sani wannan aiki ba sauki ne da shi ba. Da yawa wadanda suke amfani ‘yan kadan din baso suke a sama canji ba so suke a ci gaba da tafiya a haka.  Burinsu shi ne a ci gaba da yadda ake yi wato  a ci gaba da sace mutane a Zamfara da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna dama sauran jihohin Arewa gaba daya, su a wurin su haka ta yi  musu daidai duk da cewa akwai yawan mutane amma ‘yan kadan sun washe komai  gaba daya.

Mun gode kwarai da gaske

Nima na gode

NDC
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden

MASU ALAKA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
Tattaunawa

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

August 28, 2026
Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattaunawa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

August 20, 2026
Nijeriya
Tattaunawa

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

August 8, 2026
Next Post
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
NDC

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
NDC

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.