Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin na matukar Allah wadai da mummunan matakin Japan dangane da batun haikalin Yasukuni, ta kuma gabatar da kakkarfar adawar diflomasiyya, da korafi mai karfi ga bangaren Japan.
Mao Ning, ta bayyana hakan ne a Litinin din a birnin Beijing, yayin taron manema labarai na rana-rana da aka saba gudanarwa, bayan da firaministar Japan Sanae Takaichi ta aike da hadaya, da gudunmawar kudi ga haikalin Yasukuni a ranar Asabar 17 da yau Litinin 19 ga watan nan na Oktoba, kana jerin jamian gwamnatin Japan, da manyan jamian jamiyyar LDP, da yan majalisun dokokin kasar suka ziyarci haikalin cikin yan kwanakin baya bayan nan.
Mao, ta jaddada cewa haikalin Yasukuni, wuri ne da aka binne ajin farko na muggan jamian Japan su 14, dake da alhakin aikata laifukan yaki a lokacin yakin mamaya da ya shude.
Jamiar ta kara da cewa, a bana ake cika shekaru 80 da bude shariun birnin Tokyo, don haka ta kara jaddada matukar bukatar Japan, da ta fuskanci tarihi, ta yi duba dangane da laifukanta, kana ta dakatar da mayar da hannun agogo baya dangane da batutuwan tarihi, ta aiwatar da matakai na hakika, wadanda za su samar mata da amincewar makwaftanta na Asiya da ma sauran sassan kasa da kasa.
(Saminu Alhassan)














