Sojojin Operation Safe Haven da ke aiki a Filato sun ƙi karɓar cin hancin Naira miliyan 13 da wasu mutum biyu da ake zargi da ta’addanci suka yi ƙoƙarin basu domin su gudu.
Daraktan yaɗa labaran tsaron ƙasa, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya bayyana nasarorin da dakarun suka samu daga ranar 9 zuwa 16 ga Yuli, 2025.
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 20, Sun Ƙona Gidaje A Ƙauyukan Filato
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sa-kai Sama Da 70 A Filato
A cewarsa, Sojojin sun samu kiran gaggawa game da harin ‘yan ta’adda a hanyar Jos zuwa Sanga a ƙaramar hukumar Sanga, inda suka ci karo da mutanen cikin mota. Bayan an tsare su, sai suka yi ƙoƙarin ba Sojojin cin hanci, amma Sojojin suka ƙi karɓa tare da cafke su.
Sojojin sun kama mutum biyun, sun kwace bindigu, da alburusai, da motar da kuma kuɗin da ya kai Naira 13,742,000. Yanzu haka ana ci gaba da bincike yayin da duk kayan da aka kwace ke hannun dakarun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp