Sojojin Nijeriya na runduna ta 3 dake jihar Filato sun kama wasu waɗanda ake zargin suna sayar da makamai da kuma yin garkuwa da mutane a yankunan Marit Mazat da Barakin Gangare na karamar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato.
An kama mutanen biyu – Saeedu Haruna da Yahaya Adamu – tare da kwato bindigar AK-47, da bindiga ɗaya da wayar ƙarama a hannunsu.
- Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato
- Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2
Mai magana da yawun Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana cewa an kama waɗannan mutane ne sakamakon wani aikin leken asiri da Sojojin suka yi tare da wata hukuma ta leken asiri a safiyar ranar 11 ga Mayu, 2025.
Binciken ya nuna cewa waɗannan mutane da ƙungiyar su suna da hannu a wasu laifuka da dama a yankunan Gashish da Kurra na Filato da kuma Gwantu da Fadan baya bayan nan na ƙaramar hukumar Sanga a jihar Kaduna.
Hukumar ta yaba da yadda jama’a ke ba da gudunmawa wajen gano wuraren da ‘yan daba ke amfani da su, inda ta kuma yi kira ga jama’a da ci gaba da ba da bayanai masu aminci don taimakawa wajen warware matsalolin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp