Rundunar Sojin Saman Nijeriya, ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan rahotannin da ke cewa fararen hula 16, ciki har da ‘yan sa-kai, sun rasa rayukansu a harin sama da aka kai a ƙauyen Tungar Kara da ke Jihar Zamfara.
Rahotannin sun nuna cewa harin, wanda aka kai don fatattakar ‘yan bindiga, ya afka wa wasu ‘yan sa-kai na Jihar Zamfara da fararen hula waɗanda suka haɗu domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
- Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Makaranta Kyauta Ga Dalibai 789,000
Mai magana da yawun rundunar, Olusola F. Akinboyewa, ya ce sojin sama na ɗaukar rayukan ‘yan Nijeriya da muhimmanci.
Ya kuma tabbatar da cewa za a yi cikakken bincike kan lamarin domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma sanar da jama’a sakamakon binciken.
A nata ɓangaren, gwamnatin Jihar Zamfara ta nuna alhininta ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa harin ya afka wa ‘yan sa-kai da aka ɗauka ‘yan bindiga ne, yayin da suke ƙoƙarin kare jama’a daga hare-haren ‘yan bindiga.
Kurakuran Irin Waɗannan Hare-hare A Baya
Irin wannan kuskuren ba sabon abu ba ne a yaƙin da ake yi da ta’addanci a Nijeriya.
A shekarar 2023, wani harin sama ya afka wa taron Maulidi a Tudun Biri, da ke Jihar Kaduna, inda aka rasa rayukan mutum 85.
Haka kuma, a 2017, harin sama ya kashe mutum 112 a sansanin ‘yan gudun hijira a Rann kusa da iyakar Nijeriya da Kamaru.
Waɗannan lamura sun ƙara nuna ƙalubalen da hukumomin tsaro ke fuskanta wajen tantance mayaƙa da fararen hula, lamarin da ke haifar da mummunan asarar rayuka.
Wannan yana buƙatar sake nazari kan yadda ake gudanar da hare-haren sama don rage irin wannan iftila’i.