Sojojin Sun Yi Juyin Mulki A Kasar Guinea Konakry

Rahotanni daga kasar Guinea Konakry sun tabbatar da sojojin kasar karkashin Laftanar Kanar Mamady Doumbouya sun kwace mulki daga hannun Shugaban Kasar Alfa Konde a yau Lahadi. Tunda safiyar yau aka ji karar harbe-harbe a zagayen fadar Shugaban Kasa dake birnin Konakry.

An ga hotunan Sojoji a yayin da suka kama Shugaban Kasa Alfa Konde, inda gungun sojojin suke yawo a dukkan manyan tintunan kasar ta Guinea.

Wasu majiyoyin suna cewa dakarun sojin kasar masu biyayya ga Alfa Konde sun kama dakarun da ke goyon bayan juyin mulkin har su 25, zuwa yanzu babu tabbacin me yake faruwa a kasar saboda yadda majiyoyi suka sha bam-bam.

Exit mobile version