Ta Kone Kishiyarta Kurmus A Neja

Daga Sulaiman Ibrahim

Wata uwar gida a Minna Ta Jihar Neja ta lakada wa kishiyarta duka har lahira sannan kuma ta kone gawar kurmus.

Fatima wacce ta rigamu gidan gaskiya Amarya ce ‘yar asalin jihar katsina, Lamarin ya faru ne a jiya Talata, kwanaki 55 kenan da daura mata aure a watan Janairun da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa kishiyoyin biyu ba a gida daya suke zama ba, sai dai zafin kishi ya sanya Amina uwar gida tai wa Fatima Amarya takakka har gida inda da bayan ta lakada mata duka ta rufe ta a daki sannan ta cinna wa gidan wuta.

Wani dan uwan Marigayiyar mai suna Malam Jamilu ya ce, “tun da karfe 10 na safe zuwa daya na rana duk munyi magana da ita, amma daga karfe 3 zuwa 4 na Yammci mummunan labari mai kada zuciya da hanta wanda ba zan taba mantawa da shi ba har karshen rayuwata ya same ni cewa uwar gidan Fatima wato Amina ta hadu da kannenta sun yi mata dukan tsiya da tabarya.”

Exit mobile version