Ta’aziyyar Dr. Muhammad Uba Adamu (Kantoma) 1935-2020

Ta’aziyyar Dr. Muhammad Uba Adamu (Kantoma) 1935-2020

Daga Ibrahim Sheme

 

Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!

A jiya Litinin, 27 ga Afrilu, 2020 Allah (swt) ya yi wa Dakta Muhammadu Uba Adamu, tsohon Kantoman Kano, rasuwa. Mutumin unguwar Daneji cikin Birnin Kano ne, amma gidan sa na Kawo Bus Stop a Nassarawa, kusa da unguwar Giginyu.

Ya rasu da misalin karfe 6:40 na yamma, daf da shan ruwa, a Asibitin Nassarawa, Kano. Ya bar mata biyu, ‘ya’ya 17 da jikoki fiye da 54.

Babban dan sa shi ne Farfesa Abdalla Uba Adamu, Mataimakin Shugaba (Bice-Chancellor) na Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (National Open Unibersity of Nigeria, NOUN) wadda ya karbi ragamar jagorancin ta a shekarar 2016,  kuma zai kare wa’adin sa na shekara biyar a Fabrairu, 2021.

Iyalan marigayin sun ce bai yi wata cuta, jinya ko rashin lafiya ba, sai dai tsufa. Tashi daya abin ya zo masa da safe, Allah ya karbe shi daf da shan ruwan azumin ranar 4 ga Ramadan. Sun ce a rayuwar sa gaba daya, sau hudu ya taba kwanciya a asibiti. Wannan kwanciyar ita ce ta hudun, kuma ta karshe.

An haifi Dakta Muhammadu Uba Adamu a Daneji a ranar 10 ga Disamba, 1935, a gida mai lamba 147, wadda yanzu ta koma lamba ta 97. Watau dai ya rasu ya na dan shekara 85 kenan.

Shi ne na uku a cikin ‘ya’ya biyar da su ka rayu wadanda iyayen su su ka haifa. Sauran, ban da kanin sa, Alhaji Danbala Adamu, mata ne, kuma duk Allah ya yi masu rasuwa da jimawa.

Marigayin ya fara karatun sa na boko a ‘Shahuci Judicial School’, daga nan ya tafi ‘School for Arabic Studies’, sannan sai kuma ya tafi ‘Abdullahi Bayero College’ wadda ta zama Jami’ar Bayero, Kano, wadda kuma ya gama a 1968 da digirin farko a fannin Tarihin Siyasa (Political History).

Ya je Jami’ar Ife da ke Ile Ife (wadda yanzu ake kira Jami’ar Obafemi Awolowo) inda ya yi gajeren kwas a kan nazarin Mulkin Jama’a (Public Administration).

Tun Malam Muhammadu ya na makaranta ya ke da sha’awar rubuce-rubuce, a inda ya rubuta wata makala mai taken ‘Some Notes on the Influence of North African Traders in Kano (1968), aka buga ta a mujallar ‘Kano Studies’. A cikin ta, ya yi bayani a kan yadda Larabawan Libya, Misira da Marokko mazauna Kano su ka mamaye Kano da al’adun su na darika da kuma ire-iren abincin su da tufafi, har Hausawa su ka mayar da su nasu.

An nada shi Di’o (District Officer) na Dambatta a cikin 1969, watau a zamanin mulkin Gwamna Audu Bako. A 1970 aka nada shi Kantoman Kewayen Kano (Kano Local Authority), wanda hakan ya sa ya zama kamar Magajin Gari.

A zamanin sa ne aka yi gyaran Kano sosai, aka kuma zamantar da ita, kuma shi ya jagoranci kwamitin mayar wa da kabilar Ibo kadarorin su da aka dinga wawaso lokacin yakin Biyafara (1967-1970) a Sabon Garin Kano, kuma ya tabbatar da an mayar wa da kowa hakkin sa.

Saboda irin aikin da ya yi ne ya sa shahararren marubucin wakokin nan, marigayi Dakta Akilu Aliyu, ya rubuta masa wakar yabo a 1971 mai suna ‘Zan Je Ziyarar Shugaba Dattijo Kantoma Uba’. Ya rubuta ta ne da ajami kuma ya kai wa Kantoma ita har gida a cikin 1974 saboda jinjinawa.

Dakta Muhammadu Uba Adamu ya bar aikin Kantoma a 1975, sannan ya tafi Unibersity of Pennyslbania da ke Amurka ya karo digiri na biyu a cikin 1976. Da ya dawo aka nada shi Babban Malami (Senior Lecturer) a fannin Mulkin Jama’a (Public Administration) a ‘School of Management’, Kano a Janairu 1979. Ya na aikin ya yi rijistar digiri na uku, watau PhD, a Jami’ar Bayero a fannin Kimiyyar Mulki (Political Science) inda ya gama a 1995.

Ya yi ritaya daga aikin gwamanati a cikin 1995 ya na da shekaru 60, wato jim kadan da gama karatun sa na PhD, domin ya yi karatun ne da ma domin kara wa kan sa ilimi, ba domin neman cigaba wajen aiki ba.

Bai tsaya a nan ba, sai ya shiga rubuce-rubucce. Littafin da ya fara rubutawa shi ne ‘Confluences and Influences: The Emergence of Kano as a City State’ (1999). Littafin ya samu karbuwa, saboda haka nan da nan ya kare. Yanzu haka Farfesa Abdalla na da niyyar sabunta littafin domin fitowa da shi a badi.

Amma saboda muhimmacin littafin wajen tarihin Kano, sai Hukumar A Daidaita Sahu, a yadda ta ke a wancan lokacin, ta dauki alkawarin cewa in ya fassara littafin zuwa Hausa, su kuma za su daukin nauyin ganin an yi dab’in littafin a madaba’ar ta gwamnatin Kano, ba sai ya biya ba. Nan da nan ya fara aikin fassara da kuma karin bayani a kan wancan na Turancin. Kuma ya dinga kai fassarar Jami’ar Bayero saboda kwararru su inganta ta.

Daga bisani Hukumar A Daidata Sahu ta buga sakamakon a littattafai guda biyar a 2007 masu  taken ‘Kano Kwaryar Kira Matattarar Alheri’.

Wadannan su ne:

Kashi na 1: Kano Daga Dutsen Dala;

Kashi na 2: Kano Daga Kwazazzabon ‘Yar Kwando;

Kashi na 3: Kano Da Makwabtan Ta;

Kashi na 4: Kano Daga Garko;

Kashi na 5: Kano Daga Dutsen Bompai.

Sannan ya na bincika takardun sa sai ya ga wakar Akilu Aliyu a 1974. Sai ya fara tunanin yin abubuwa biyu – rattaba tarihin abin da ya jawo wakar, watau ayyukan da su ka yi na gyaran birnin Kano, lokacin marigayi Gwamna Audu Bako, da kuma waken ayyukan. Duk ya hade su a littafin da ya rubuta mai suna ‘Tuna Baya’ (2009).

Hukumar KNUPDA ta Kano ita ta dauki nauyin buga littafin. Amma bai yi wannan ba sai da ya gama rubuta littattafan ‘Kano Kwaryar Kira Matattarar Alheri’ wanda A Daidaita Sahu’ ta dauki nauyin sa.

Bayan wadannan, ya rubuta ‘Sabon Tarihin Asalin Hausawa’ (2011), inda ya danganta Hausawa da wani Fir’auna mai suna Housal a Misra wanda ya taho da mutanen sa, abin da ya zama kasar Hausa daga baya.

A cikin 2011 sai Allah ya sa su ka hadu da shahararren fasihin mawakin nan, Aminudeen Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da ALA a Zoo Road, Kano. Bayan ALA ya gaishe shi, sai Kantoma ya ce ai shi ma ya na rubuta wakoki amma ba shi da muryar da zai rera. Nan take ALA ya ce shi zai yi. Su ka koma gidan Kantoma inda shi Kantoman ya bai wa ALA wakokin sa na gyaran Kano. ALA ya shiga situdiyo ya yi abin da ya saba – wato rera wakoki cikin natsuwa. Sakamakon shi ne faifan sidi mai suna ‘Duniya Makaranta’, wanda ya kunshi wakoki kamar haka:

  1. Bolar Kano (24:34)
  2. Hassada (10:47)
  3. Badar (20:59)
  4. Dan Maraya (12:49)

Idan akwai wani abu da ya ke faranta wa marigayi Dakta Muhammadu Uba Adamu rai a rayuwa, shi ne wadannan wakokin wanda har ya kusan komawa ga mahaliccin sa ya na sauraron su da na’urar ‘MP3 player’. Idan ya na sauraro, sai a ga fuskar sa cike da kwanciyar hankali domin tunawa da baya da kuma jin dadin yadda ALA ke fito da ainihin abubuwan da su ka faru a cikin baitukuan.

Allah ya gafarta ma sa da rahama, amin.

 

Marigayi (Dr.) Uba Adamu (hagu) da babban xansa, Farfesa Abdalla Uba Adamu, a watan Janairu na 2017 (Hakkin hoto: Abdulrahman Abdullahi).

Exit mobile version