Kasar Sin na kiyaye wata al’ada ta tsawon shekaru 35 a fannin diflomasiyya, wato a farkon kowace shekara, ministan harkokin wajen kasar kan yi ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka. A wannan shekara ma haka aka yi, inda daga ranar 5 zuwa 11 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Namibia da Congo Brazzaville da Chadi da ma Nijeriya, bisa goron gayyatar da aka yi masa.
Wani abokina dan Nijeriya ya taba min tambaya, shin me ya sa ministocin harkokin wajen kasar Sin suka yi ta kiyaye wannan al’ada? Muna iya gano amsar tambayar daga zancen da Mr.Wang Yi ya yi lokacin da yake ziyara a kasar Namibia. A yayin zantawa da shugabar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah, Wang Yi ya ce, ”Ta hanyar kiyaye wannan al’ada ta kai ziyararmu ta farko a kasashen Afirka a farkon kowace shekara, muna son shaida wa duniya cewa, a duk irin sauye-sauye ko yanayin da ake ciki a duniya, kullum kasar Sin za ta kasance aminiyar da kasashen Afirka suka yi amanna da kuma dogaro da ita a kokarinsu na tabbatar da ci gabansu, haka kuma kasa ce da ke mara musu baya a dandalin kasa da kasa. ”
- Zargin Safarar Kananan Yara: Gwamnatin Kano Ta Karbi Yara 59 Da Aka Kama A Hanyar Zuwa Nasarawa
- An Nemi Sojoji Su Kara Jajircewa Wajen Gudanar Da Ayukansu
Yadda kasar Sin ta furta ke nan, kuma hakan take aikatawa. Idan ba mu manta ba, a zamanin da kasashen Afirka ke gwagwarmayar neman ‘yancin kansu, kasar Sin ta nuna tsayayyen goyon bayanta tare da samar da gudummawarta gare su. Bayan da suka samu ‘yancin kansu kuma, kasar Sin ta ci gaba da tallafa musu a kokarinsu na kiyaye ikon mulkin kansu da kuma raya tattalin arzikinsu. Ya zuwa karshen shekarar 2023, yawan kudaden jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen Afirka ya zarce dala biliyan 40, ta kuma taimaka wajen gina hanyoyin mota na tsawon kilomita dubu 100 da layukan dogo na sama da tsawon kilomita dubu 10 da gadoji kusan dubu da ma tashoshin jiragen kasa kusan dari a Afirka. Haka nan, ko a cikin shekaru 3 kadai da suka wuce, ta samar da guraben aikin yi fiye da miliyan daya a Afirka. Kasar Sin ita ce ta farko da ta bayyana goyon bayanta ga shigar da kungiyar tarayyar Afirka a matsayin mamban kungiyar G20. Lallai jerin nasarorin da aka cimma sun shaida huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma yadda kasar Sin take cika alkawuranta a kullum ya kasance sanadin dimbin nasarorin da aka cimma.
A gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka(FOCAC) da ya gudana a watan Satumban bara a birnin Beijing, kasar Sin da dukkanin kasashen Afirka da suka kulla huldar diflomasiyya da ita sun sanar da daukaka huldarsu. To, wannan sabon mafarin huldarsu ya sa ziyarar ministan wajen kasar Sin kasashen Afirka a wannan karo ya sha bamban da na baya, wato ziyarar na da nufin tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin dandalin FOCAC, da kuma kara inganta hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.
Don haka, bayan da ya gana da shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso, Wang Yi ya ce, ”Dalilin wannan ziyara shi ne don mu tattauna tare da Congo Brazzaville, domin mu cimma daidaito a kan yadda za a kara inganta hadin gwiwarmu karkashin tsarin dandalin FOCAC. ” An ce, bayan tattaunawa tare da Congo Brazzaville, wadda ta kasance kasar da ke shugabantar dandalin FOCAC tare da kasar Sin a wannan karo, sassan biyu sun tsara jadawali da ma taswira game da tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron dandalin FOCAC nan da shekaru uku masu zuwa. Misali, a bana, sassan biyu za su kira taron ministoci na tabbatar da sakamakon taron dandalin, don sa kaimin cimma nasarorin hadin gwiwarsu da wuri. Sa’an nan a shekarar 2026, sassan biyu za su gudanar da bukukuwa na murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka da musayar al’adu a tsakaninsu, haka kuma za a kira taron manyan jami’ai karo na 18 na dandalin FOCAC, don gaggauta tabbatar da sakamakon da aka cimma.
Har wa yau, a lokacin ziyararsa, Wang Yi ya ce, kasar Sin na son sa kaimin aiwatar da shawarar kiyaye tsaron duniya ta yadda za ta haifar wa Afirka da mai ido. ”Za mu kulla kawance da kasashen Afirka wajen tabbatar da shawarar kiyaye tsaron duniya, tare da sa kaimin aiwatar da shirin hadin gwiwar kiyaye tsaro. Za mu samar da gudummawar soja na yuan biliyan ga kasashen Afirka, tare da taimaka wa kasashen Afirka horar da kwararrun soja 6,000 da ‘yan sanda 1,000…”, in ji shi. Ban da haka, ya ce, kasar Sin tana so hada kai da kasashen Afirka wajen tabbatar da shirin samar da makamashi mai tsabta da aka gabatar a gun taron kolin dandalin FOCAC, da raya ayyukan samar da wutar lantarki ta makamashin hasken rana, don taimaka wa kasashen Afirka tabbatar da bunkasar tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba.
Kyan alkawari cikawa, kullum kasar Sin na cika alkawuranta na tallafa wa kasashen Afirka wajen tabbatar da ci gabansu. Bisa wannan ziyarar ta ministan harkokin wajen kasar Sin a kasashen Afirka, an tsara jadawali da taswira game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka nan da shekaru uku masu zuwa, kuma tabbas hadin gwiwarsu zai kara haifar da da mai ido a yayin da suke kokarin zamanantar da kansu. (Lubabatu Lei)