- Za Mu Tabbatar Da Cikakken Tsaro —KADCIMMA
| Daga Bello Hamza,
An bayyana cewa, kasuwar baje kolin duniya ta Kaduna da za a ci a bana za ta samu karin tagomashi fiye da na baya sosai bisa kwararowar kasashen waje da sauran manyan ‘yan kasuwa na duniya. Har ila yau an nunar da cewa an kammala dukkan shirye-shirye musamman a kan abn day a shafi bangaren samar da tsaro don ganin an samu nasarar gudanar da bikin baje kolin masa’anantu da aka saba yi duk shekara a filin baje koli da ke Rigachikum Kaduna.
Babban Darakta na Majalisar ‘yan Kasuwa, Masa’anatu da Albakun Gona (KADCCIMA) na Jihar Kaduna, Alhaji Usman Garba Saulawa bayyana haka a tattanawarsa da Wakilimu jim kadan bayan shugabannin majalisar suka kawo wa Kamfanin Jaridar Leadership Hausa ziyara a babban ofishinta dake Abuja ranar Laraba.
Ya kuma kara da cewa, Majalisar Masa’anantun na da dogon tarihi da kamfanin Jaridar Leadership, “Ta yadda suke tallata tare da yayata harkokinmu, musamman a wannan karon da muke shirin gabatar da kasuwar baje koli na duniya karo na 43 a nan Kaduna daga ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa 6 ga watan Maris 2022, muna bukatar kamfanin Leadership ta taimake mu wajen yayata harkokin da za mu gabatar kafin taron da yayin gudanar da taron kuma ta bamu shawarwari bayan taron don gyara tare da kara azama a shirin mu na shekaru masu zuwa” in ji shi.
Babban Daraktan ya kuma sanar da cewa, zuwa yanzu sun samu nuna sha’awar shiga shirin daga kasashe na duniya da dama kamar su Moroko, Masar, Insland, Birtaniya da wasu kasashe a nahiyar Asiya, yayin da kuma zuwa yanzu jihohi da dama da kamfanoni masu zaman kansu da masu zuba jari daga ciki da kuma kasashen waje sun bayyana aniyarsu na shiga taron baje kolin, wanda shi ne mafi shahara a Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewa, a wannan karon an tanadi wasu shirye-shirye masu kayatarwa, da suka hada da kacici tsakanin ‘yan makarantu, za kuma a bayar da kyaututtuka ga wadanda suka nuna bajinta. Daga nan ya kuma bayyana cewa, sun yi cikakken shiri a bangaren tsaro don ganin an gudanar da biki cikin nasara, “Kwamitin tsaro a karkashin shugabancin Kanal Jibrin Hassan (Sarkin Yakin Hadeja) ya yi dukkan shiri na ganin an samar da issashen jami’an tsaro don ganin ba a samu wani barazana ba kafin da yayin gudanar da taron” in ji shi.
Daga nan ya ce, suna samun dukkan goyon baya daga gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru El-Rufa’i. Cikin tawagar da suka kawo ziyarar akwai Alhaji Sulaiman Aliyu, Alhaji Faruk Sukaiman da Kanal Jibrin Hassan (Sarkin Yakin Hadejia).