Daga Bello Hamza
Wani dan siyasa kuma mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara a fannin ci gaban a’lumma, Honarabul Hambali Shiitu Samaho, ya bayyana cewa, babban kudirinsa a kowane lokaci shi ne tallafawa alumma musamman matasa ta fannin Samar da aikin yi da guraben karatu a makarantun ciki da wajen jihar, Honarabul Hambali Wanda kuma shi ne mai ba Gwamnan jihar Zamfara shawara a bangaren ci gaban alumna ya yi wannan bayanin ne a wata tattaunawa da ya yi da LEADERSHIP A Yau a ofishinsa dake Gusau , daga nan ya jawo hankalin ‘yansiyasa da su mayar da hankali wajen taimakawa matasa “ domin su ne kashi bayan alumna” in ji shi.
Daga nan Honarabul Hambali ya jinjinawa gwamnatin jihad karkashin jagorancin Allaji Yari a kan kokaeinta da tsare-tsarenta na bukasa rayuwar matasa a fannin Samar da ilimi da sana’o’i “ hakan zai taimaka wajen Samar da matasa masu dogaro da Kansu” saboda haka, sai ya bukaci matasa da su rungumi wadannan kudurori na gwamnati domin samun cikakkiyar nasara, ya kuma bukaci matasa da su rungumi akidar zama lafiya.