A rahoton da Gidauniyar Tunawa da Sa Ahmadu Bello ta fitar kwanan nan bayan babban taron da ta yi a Abuja, ta bayyana takaicinta a kan tabarbarewar ilimi da rashin kwarewar Malamai a yankin Arewacin Nijeriya. Duk da cewa, kamar bayanan ba wani abu ne sabo da jama’a da dama ba su sani ba, amma dole abin ya tayar da hankali musamman ga duk wani da yake yi wa yankin fatan alhairi. Rahoton ya bayyana cewa, kashi 50 na malaman da ke karantarwa a Arewa ba su cancanta ba don kuwa ba su da mafi karancin shaidar ilimi da doka ta amince da ita ta NCE.
Wannan bayani mai tayar da hankalin yana zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar duniya ta ware rana ta musamman don bikin ranar Malamai inda ake bada gudummawarsu ga kokarin samar wa da kasa ingantattun ma’aikata don bunkasa kasa gaba daya. Malamai sune masu raino don samar da shugabanni a dukkan bangarorin rayuwar al’umma gaba daya, a saboda haka dole su zama abin koyi ga yara masu tasowa.
- ‘Ya’ya Mata Miliyan 7.6 Aka Tauye Wa Samun Ilimin Boko A Nijeriya — UNICEF
- Ilimin ‘Ya’ya Mata: Kano Ta Fara Bai Wa ‘Yan Mata 45,000 Tallafin N20, 000
Taron wanda ya samu halartar masu fada a ji da masu ruwa da tsaki a harkokin da suka shafi Arewacin Nijeriya sun kuma bayyana cewa, yawancin wadanda suka samu kansu a harkar karantarwa a Arewa ba sun shiga ba ne saboda suna kaunar sana’ar amma sun shiga ne saboda basu samu wani abin yi ba ne, amma da zarar sun samu wani abin yi sai su watsar da aikin karantarwar. Abin da wannan yake nunawa shi ne harkar karantarwa ta zama wani fage na zuba tarkacen mutanen da suka kasa samun nasara a wasu bangarori na rayuwa. Wannan wani abin tashin hankali ne.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin shugabancin Nasir el-Rufa’I ta kori malamai 2,357 wadanda suka fadi jarabawar da aka yi musu. A lokacin hukumar kula da Ilimin Firamare (KADSUBEB) ta shirya wa malamai 30,000 jarabawa, yawancin su suka kasa cin jarabawar dalilin da ya sa aka kore su.
Ya kamata a fahimci cewa, lamarin malamai da basu kware ba a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu ba abu ba ne da ya takaita a yankin arewacin Nijeriya kawa ba, abu ne da ya karkade bangaren ilimin kasar gaba daya, sai dai kawai lamarin ya fi yawa ne a yankin Arewacin Nijeriya.
A ra’ayinmu, wannan tabarbarewar a bangaren harkar ilimi abu ne da ya shafi yadda shugabanni ke tafiyar da mulki da kuma yadda suke kasa muhimmantar da harkar ilimi a jadawalinsu.
Wani bangare na matsalar shi ne yadda sana’ar koyarwa ya zama baya samun muhimmanci daga ‘yan siyasanmu inda suka mayar da shi wani waje na jibge magoya bayansu da basu da wata makoma, kamar wadanda suka shirya watsarwa bayan an kammala gwagwarmaryar siyasa, suka kasa sanin yadda za su yi da su, sai su tura su azuzuwa a matsayin malamai. Kuma saboda dalilai na siyasa babu wanda ya isa ya yi magana ciki har da kungiyar malamai ta NUT, su kan kawar da kai su nuna kamar basu san abin da ke faruwa ba.
Wata babbar matsalar a nan ita ce yadda wasu gwamnoni a yankin Arewa suka kasa samar da tsarin da zai kai ga horas tare da samar da kwararrun malaman da ake bukata a yankin ta hanyar samar da issasun kudade ga makarantun horars da malamai da ake da su a yankin. Idan har babu wannan, zai zama tamkar munafinci ne irin koke-koken da aka yi a kan rashin kwararrun malamai a yankin arewa, kamar yadda aka yi a taron da aka yi a Abuja kwanan nan.
A matsayinmu na gidan jarida, muna bukatar ganin gwamnatocin jihohi a Arewacin Nijeriya su gaggauta daukar matakin rage yawan malaman da su da kwarewar da ake bukata, maimakon su zauna suna koke-koke wanda ba zai taba maganin halin da ake ciki ba.
Dole a samar da hanyoyin tabbatar ana samun kwararrun malamai, in har ba a yi haka tamkar ana kwangaba-kwanbaya ne, samar da matasa masu ilimi na cikin hanyoyin yaki da matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa. Ya kuma kamata a lura da cewa, in har babu kwararrun malamai za a dinga tura wadanda suka kammala makaranta ne da ba za su iya fuskantar wani aiki ba a rayuwarsu saboda basu da ilimin da ya kamata.
A kan haka ya kamata masu tafiyar da mulki a dukkan matakai su samar da hanyoyi na musamman da zai kai ga kara yawan kwararrun malamai. Wannan kuma abu ne da ya kamata a yi da gaggawa saboda muhimmancinsa.
Matsalolin da ilimi ya shiga a arewa ya faro ne tun lokacin wadanda ke ikirarin kasancewa tare da Sa Ahmadu Bello suka yi watsi da akidarsa na sa yankin a gaba, musamman akidarsa na bunkasa ilimi.
Hanya farfado da harkar ilimi a mahangarmu shi ne, shugabanni a arewa da sauran bangarorin Nijeriya su koma tushe ta hanyar samar da sabbin hanyoyin da za su bunkasa bangaren ilimi wadanda suka hada da zuba jari mai yawa wajen horas da malamai da kuma horas da su a kai akai.