Yusuf Shuaibu" />

Tallafin Gwamnatin Tarayya A Kan Bunkasa Noman Tumatur Ya Kai Naira Biliyan 10

Babban bankin Nijeriya ta bayyana cewa, ta saka naira biliyan 10 a kan bunkasa noman tumatur a kan ayyuka guda takwas. Ta bayyana cewa, daya daga cikin ayyukan su ne, ‘Dangote Green House Tomato Manufacturin Project’, yana iya noma irin tumatur miliyan 10 a duk wata. Babban bankin ya ce, wannan zai iya sa a saida kamar 5,000, wanda zai girma sannan a mika su zuwa kamfanoni wanda za su aiki cikin kananan makonni tare da kayan marmari na tumatar.
Ta kara da cewa, wannan aiki zai iya samar wa mutane miliyan daya aikin yi daga kananan manoman tumatur. Babban bankin ya ce, wannan aikin zai iya bunkasa tattalin arzikin Nijeriya wanda ya kai dala miliyan 250 ga kowani shekara.
Gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, bankin ya kara bunkasa harkar noma da kuma masana’antu, ta hanyar bunkasa kananan kasuwanci da shirin bayar bashin da kuma bayar da tallafin noma.
“Musamman da muka kara bunkasa kayayyakimu guda hudu (Shinkafa, Kifi, Suga da Alkama), wadanda ake cinye naira tiriliyan 1.3 kudin shigowa da su cikin wannan kasa a kowani shekara,” in ji shi.
Domin karfafawa sauran bankuna wajen bunkasa harkokin, ya ce, a watan Yulin shekarar 2018, babban bankin ta hannun kwamitin tsare-tsaren kudaden, ya yi alkawarin zai bai wa bankuna wasu kudade bisa wasu dalilai. “Bankunan za su kawo sabon tsari a kan bunkasa noma da masana’antu, bankin zai goyi bayansu dari bisa dari,” in ji shi.
Bankin ya ce, ana fatan bankunan za su yi amfani da wannan dama domin kara fadada basussukansu a kan masana’antu.
Emefiele ya ce, karyewar da gangan man fetur da ya yi a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017, wannan ya yi tasiri a tattalin arzikin Nijeriya,” in ji shi.
“Yana da muhimmanci mu samar da wani tsari ko kuma shiri wanda zai bunkasa tattalin arziki domin rage dogaro da kayayyakin kasashen waje,” in ji shi.
Ya ce, bunkasa sauran fannin noma zai ci gaba da rage matsalar aikin yi. “Tsarin yana cikin kasafin kudi wanda zai tallafa wa manona da kuma masu aiki a kafanin yadi domin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya,” in ji Emefiele.

Exit mobile version