An haifi Hajiya Hajaratu Gambo Sawaba a shekarar 1933 a birnin Zariya, Jihar Kaduna. Sunan Mahaifinta, Isaac Dakwada, wanda shi ɗan asalin ƙasar Ghana ne, yayin da kuma ita mahaifiyarta da ake kira da suna Fatima ta fito ne daga cikin kabilar Nupawa. Yarintarta ko nace ƙuruciyarta ta cika da nauyin da ya fara yi mata yawa tun da wuri, bayan rasuwar mahaifinta tana ƙarama, sannan kuma da mutuwar mahaifiyarta ba da jimawa ba.
Tun tana yarinya, Hajiya Gambo wadda ta saba da yin gwagwarmaya, inda ta nuna ƙarfin hali da kuma nuna shi ’yanci wani abu ne mai daɗi. Ta yi karatu a ne a Makarantar Natiɓe Authority da ke Tudun Wada, Zariya, amma iliminta ya tsaya ne bakin iyakar Firamare a sanadiyar auren da aka yi mata tun tana kusan ‘yar shekara 13—wannan kuma a wancan lokacin wani abu da ya zama ruwan dare game duniya a Arewacin Nijeriya. Ko da yake auren da tayi bai daɗe ba, wannan ne ya buɗe mata ido kan buƙatar cewa mata suna da ’yancin su yi zaɓe kai har ma suna iya zama wakilan al’umma a majalisu, wannan kuma ta ɓangaren harkar siyasa ne.
- Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar
- Sin Na Maraba Da ’Yan Jaridar Duniya Da Su Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Harin Japan Da Na Tafarkin Murdiya
Rayuwarta ta sirri ta shahara da aure-aure masu yawa inda har sai da ta yi aure har sau biyar baki ɗaya inda kuma mijinta na huɗu, ana kiransa da suna Abubakar. Duk da cewa aurarrakain da ta yi sun kasance da manyan matsaloli na ƙalubale, ita ce ta ke ɗaukar gabarar ɗawainiyarsu data tafiyar da gida, haka ta haɗa abin ga kulawa da gida, ta waje ɗaya ga kuma lamarin gwagwarmayar siyasa wadda a wancan lokacin tana da matuƙar haɗari.
Gambo Sawaba ta shiga siyasa tun tana matashiya, inda ta zama ‘yar jam’iyyar Northern Elements Progressiɓe Union wato (NEPU), jam’iyyar marigayi Malam Aminu Kano, wadda daga baya kuma aka sauaya mata suna zuwa PRP People’s Redemption Party babbar jam’iyyar adawa ce d take da mai tsattsauran ra’ayi, da take ƙalubalantar waɗanda suke da mulki a hannunsu bama a Arewa kaɗai ba sai da ta mulki Nijeriya Jam’iyyar NPC Jam’iyyar su Abubakar Tabawa Balewa Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato da dai sauran manyan ƴan siyasa. Ta kasance ɗaya daga cikin muryoyin mata da suka fi ƙarfi a cikin jam’iyyar, tana yaɗa manufofin bai wa mata ’yancin yin zaɓe, shiga siyasa, ilimi da kuma kariya daga wasu munanan al’adun da basu zama dole sai an yi su ba.
Gwagwarmayar da take yi ne bayan data fito a filihakan yasa ta samu girmamawar manyan Shugabanni na ƙasa, ciki har da jagoran siyasar Kudu maso gabashin Nijeriya Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda ake cewa shi ne ya kira da sunan mai laƙabin “Sawaba”—abinda yake nufin ’yanci a kalmar Hausa.













